MUZGUNA WA MA’AIKATAN MU: Za mu dauki mataki – Hukumar NDLEA

0

Shugaban Hukumar Hana Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi (NDLEA) Muhammad Abdallah ya koka kan yadda mutane ke muzguna wa ma’aikatan hukumar wajen gudanar da aikin su.

Abdalla ya fadi haka ne a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Litini wanda jami’in hulda da jama’a na hukunar rundunar Jonah Achema ta saka wa hannu.

Ya ce tun da aka kafa hukumar NDLEA ta rasa ma’aikata 200 a dalilin far musu da mutane ke yi a wajen aikin su.

Abdalla yace a shekarar 2018 an kashe ma’aikatan NDLEA uku a Okene, jihar Kogi kuma a watan Fabrairun 2019 an kashe ma’aikatan NDLEA hudu a jihar Ondo.

” Haka kuma a Kazaure, jihar Jigawa, an sassari jami’in a wajen farautar masu ta’wmmali da muggan kwayoyi. Bayan haka maharan sun kona ofishin mu dake yankin sannan sun banka wa motocin da muke aiki da su a wurin wuta.

Abdalla ya kuma kara da cewa a watan Maris mahara sun kai wa ma’aikatan NDLEA hari bayan sun diran wa wani dakin bye ganyen tabar Wiwi a dajin Okpuje dake karamar hukumar Owan jihar Edo.

Abdalla ya ce hukumar na gudanar da bincike domin kama duk mutanen da suke da hannu wajen hana ma’aikatan su gudanar da aiyukkan su.

” A yanzu dai tura ya kai bango domin za mu dauki mummunar mataki wajen hukunta duk wanda muka kama yana muzguna wa ma’aikatan mu a wajen aikin su.

Abdalla ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, da jami’an gwamnati da su taimakawa hukumar wajen ganin tayi nasara a aikin da tasa a gaba.

Share.

game da Author