Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Kebbi Assad Hassan ya bayyana cewa mutane shida sun kamu da zazzabin Lassa.
Hassan ya sanar da haka ne wa manema labarai ranar Lahadi a Birnin Kebbi.
Ya ce ma’aikatar kiwon lafiya ta sami rahotanin bullowar cutar a tsakanin watannin Fabrairu zuwa Afrilu.
” Mutanen da suka kamu da cutar masu shekaru 25 zuwa 65 ne inda hudu daga Birnin Kebbi suke, biyu kuma daga karamar hukumar Bunza.
Hassan yace an kawo wata mata cikin mutane shida da suka kamu da cutar babban asibitin dake Birnin Kebbi inda likitan dake duba ta shima ya kamu da cutar.
” A yanzu dai ana duba likita, maikatan asibitin da sauran mutanen da ke kananan hukumomi 21 a jihar domin dakile yaduwar cutar.
Bayan haka Hassan ya karyata rade radin da wasu ke yadawa cewa wai wasu yara biyu sun rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Ya ce babu alamun gaskiya a wannan maganan.
A karshe Hassan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da tsaftace muhallin su da abincin su domin guje wa kamuwa da cutar.
Ga hanyoyin gujewa kamuwa da zazzabin Lassa
1. Da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan miyau, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba shi da shi.