Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC ta bayyana cew ya zuwa watan Maris da ya gabata, akwai mutane a kasar nan har miliyan 115, 938,225 masu amfani da intranet.
NCC ta ce adadin ya karu idan aka kwatanta ta miliyan 114, 726, 357 da ake da su a cikin watan Fabrairu. NCC ta ce kenan a cikin wata daya an samu karin masu amfani da intanet har milyan 1, 212, 868.
Ta ce kamfanonin AIRTEL, MTN, GLO su ne suka samu karin masu saye da kuma amfani da ‘data’ din su daga Fabrairu zuwa Maris, yayin da 9Mobile ya yi asarar mutane da yawa a cikin wata daya.
GLO ya samu karin masu sayen data har 950,115.00. Wato ya samu kari kenan daga yawan mutane milyan 27, 486, 271 da ya ke da su a cikin Fabrairu, zuwa milyan 28, 436, 386 a cikin Maris.
AIRTEL ya samu karin mutane 351, 657 cikin Maris. Kenan ya na da miliyan 31, 243, 185, maimakon milyan 30, 891, 518 a cikin Fabrairu.
MTN na da miliyan 46, 538, 633 a cikin watan Fabrairu. Amma a cikin Maris ya na da milyan 46, 552, 186. Ya samu karin 13, 522 kacal.
9MOBILE ya yi asarar masu sayen data har 166, 542 a cikin watan Maris. A watan Fabrairu ya na da mutane milyan 9, 808, 935. Amma cikin Maris ya koma milyan 9, 642, 393.
VISAFONE ya samu karin mutane 64, 076 a watan Maris. Amma a watan Fabrairu bai samu karin mutum ko daya ba.
Discussion about this post