Muna bukata a biya mu Naira miliyan 15 kafin mu saki faston LCCN – Masu garkuwa da mutane

0

Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da faston cocin LCCN Ishaku Ayuba sun bukaci a biya su Naira miliyan 15 kudin fansa kafin su sake shi.

Masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da Ayuba a gidan sa dake Badarissa karamar hukumar Girie a jihar Adamawa.

Wani cikin ‘yan uwan Ayuba da baya so a fadi sunan sa ya bayyana cewa masu garkuwan sun far wa gidan Ayuba ne ranan Laraba da karfe 1:30 na rana.

” Akalla mahara 15 ne suka kawo wa wannan mutumi hari inda suka rika harbi ta ko-ina.

” Kafin su tafi da Ayuba sai da suka ci zarafin iyalin sa. Sannan bayan sun tafi ne suka kira cewa suna bukutan a biya su Naira miliyan 15 kudin diyya.

Dan-uwan Ayuba yace cocin LCCN da iyalan Ayuba basu da yadda za su yi su iya tara wannan kudi domin biyan diyya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Othman Abubakar ya tabbatar da haka.

Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin ceto Ayuba.

Share.

game da Author