Mun kwato naira biliyan 26 cikin shekara hudu – Shugaban ICPC

0

Hukumar Hana Ma’aikatan Gwamnati Zambar Kudade (ICPC), ta bayyana cewa ta samu nasara kwato naira bilyann 26 daga 2015 zuwa yau, daga hannun jami’an gwamnati da kamfanoni.

Shugaban hukumar, Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a cikin wata hita ta musamman da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN).
Bolaji ya kara da cewa abin da aka kwato din sun hada da kudade da kuma gidaje.

Ya ce a lokutan bincike, an rika gano makudan kudade a gidajen jami’an gwamnati an kimshe.

Daga nan ya kara yin bayanin cewa ko kwanan nan an kwato gidaje har 32 a hannun ma’aikacin gwamnati daya.

“A kan samu yanayin da binciken mu kan kai mu ga kwato dukiyoyi baya ga kudade. Sai dai kuma har yanzu ba a kai ga samun nasarar yanke wa dama hukunci a kotu ba.

“Saboda ba wai da yawan mutanen da ake daurewa ba ne a ke auna nasarar yaki da cin rashawa kadai ba.

“ Idan ka dubi dokar ICPC, za ta ga cewa an ba hukumar damar tilasta bincike, kwato dudade da kadarori da kuma gurfanarwa kotu.

“Amma babban abin da ya kamata mu fi maida hankali a kan sa, shi ne hana aikata satar kudaden tun da farko.”

Ya kara da cewa, ba haka kawai jami’an gwamnati ke kwasar kudade ba. Ya ce su na hada baki da kamfanoni ne.

“Idan mu na binciken gano barnar kudade, mu na gano duk inda aka shigar da kudaden, kuma sau da yawa sai ka iske sun shiga hannun kamfanoni.

“ Idan muka bi diddigin gano kudaden sata, sai mu iske cewa da wahala ka same su a cikin asusun bankin wannan ma’aikacin da ya yi satar.

“Sai su kirkiro wasu hanyoyin satar kudade, kamar bada wasu kwangiloli, karyar karbar kudaden tafiye-tafiyen da ba su yi ba, ko kuma a karkatar da kudin da aka ce a yi wani abu da su zuwa wani wuri daban.

Sai dai kuma ya ce akan samu cewa ba dukkan zargin satar kudi ba ce a ma’aikatu da ofisoshin ma’aikatu ke zama gaskiya ba.

Share.

game da Author