Muhimman ayyukan ibada a goman karshen Ramadana? – Imam Bello Mai-Iyali

0

Bayan watanni tara a cikin mahaifiya, Allah ya zabi watan tara (Ramadan) domin tsarkake Dan Adam da kankare masa zunnubai da gafara,
don ya koma kamar yadda aka haifesa.

Dararen goman karshe na Ramadana sune mafi darajar darare ga Dan Adam, ayyukan Alhairi a cikin su suna da girman daraja fiye da sauran
darare. Goman karshe na farawa ne daga shan ruwa na rarar da azumi ya cika ashirin dai-dai har zuwa ganin watan Sallah.

Gaman karshe suna da matukan falala, Annabi yana son su, kuma yana raya su da ibada. Idan goman karshe suka zo, Annabi (SAW) yana kara
jajircewa da ibada, yana raya darairen su kuma yanisanci matansa.

MANYAN AYYUKA A KWANAKI GOMAN KARSHE

An shar’anta ayyuka masu yawa a cikin Ramadana, amma mafi girman falala su ne:

1) Neman daren Lailatul Kadari: Musulmin da yadace da wannan dare cikin ibada da imani, da ikhlasi, to ibadarsa na wannan dare kadai,
tafi alhairi da ibadar da zai yi a cikin rayuwarsa kakaf.

2) Ittikafi: shi ne lizimtar masallaci domin shagaltuwa da ibada. Hadisi ya ingata daga Imamul Bukhari da Muslim, cewa Annabi (SAW) ya
lizimci Ittikafi duk goman karshe har ya bar duniya.

3) Karatun Al-Kur’ani: Yana daga cikin manyan ibadu a goman karshe, musulmi ya shagaltu da karatunsa, cikin tunani da khushu’i da bibiyan ma’anarsa, Mala’ika Jibirilu yana bibiyan Al-Kur’ani tare da Annabi (SAW) a cikin Ramadana.

4) Yawaita Ciyarwa da Sadaka da kyauta: Mazon Allah (SAW) ya kasance kyautarsa ta fi yawa a cikin Ramadana.

5) Tsayuwar dare (Kiyamul Laili): Annabin tsira ya kasanci yana raya wadannan darare da ibada kuma yana tada iyalansa domin su yi ibada.

6) Jajircewa da Addu’ah: yawaita addu’o’i, ga kai, iyaye, iyalai da kasa. Yawaita neman gafara, da rangwame da dukkan bukatun duniya da lahira. Neman tsari daga wuta da rokon dacewa Al-Jannah.

7) Yawaita zikiri.

8) Kyautata halaye.

9) Kaucewa zalunci da kuntatawa mutane ko cutar dasu.

10) Kaucewa dukkanin sabo da zunubi, domin laifinsa yafi tsananingirma a wannan lokaci.

Ya ‘yan uwa, mu yawaita addu’ah ga wannnan kasa tamu Najeriya da mabiya da shugabanni baki daya. Ya Allah, ka yi albarka da aminci a
wannan kasa tamu Najeriya. Amin.

Share.

game da Author