MASARAUTAR KANO: Majalisar Kano za ta kirkiro sabbin manyan masaratu

0

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara sa himma wajen ganin ta kawo gyara ga dokar da ta kafa Majalisar Masarautar Kano.

NAN ya ruwaito cewa majalisar ta sake ci gaba da shirin ta na can baya, na ganin cewa ta daddatsa masarautar Jihar Kano.

Shirin ya samo asali ne daga wani korafi da ofishin Lauya Ibrahim Salisu Chambers ya shigar a Majalisa, inda ya nemi a sake kirkiro masarautu a Jihar Kano.

Kakakin Majalisar ne, Kabiru Alasan Rurum ya shugabanci zaman majalisar da kan sa jiya Litinin, kuma ya karanto takardar korafin neman kirkiro su da Salisu Chambers ya yi.

Ya ce wanda ya shigar da koken, ya nemi a kirkiro masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Ya ce kirkiro wadannan masarautu zai kawo ci gaba a yankunan, inji Ibrahim Salisu Chambers.

Mai korafin, inji Rurum, ya ce idan aka kirkiro masarautun, to mutanen karkara za su samu damar kusantowa ga gwamnatin jiha, kuma tsaro zai inganta da kuma ci gaba.

NAN ta ruwaito cewa mafi yawan mambobin majalisa sun amince da wannan batu.

Mamba mai wakiltar Karamar Hukumar Tarauni, Zakari Mohammed, ya ce wannan kokari ya zo daidai lokacin sa ake bukatar sa. Musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu jihohi suka kara kirkiro masautu.

Mambobin Takai, Dawakin Tofa, Rimin Gado, Birni Da Kewaye, Nasarawa da Tudun Wada, duk sun goyi baya.

Sun ce yin hakan zai sa a samu masarautu wadanda za su yi daidai da juna a matsayin su na sarakuna.

MAMBOBIN PDP SUN KI YARDA

Sai dai kuma mambobin jam’iyyar PDP sun yi fatali da wannan yunkuri, kamar yadda Hon. Ali Danja mai wakiltar Karamar Hukumar Gezawa ya bayyana wa manema labarai, bayan tashi daga majalisa.

Ya ce wannan yunkuri da ake yi, ba kishi ko ci gaba ba ne, siyasa ce kawai. Don haka ba za au goyi baya ba.

Share.

game da Author