MAMAYA: Gwamnan Barno ya mamayi ma’aikatan jihar, mutum 10 kacal ya samu a sakatariyar jihar cikin ma’akata 12,000

0

A wani mamayan gaske da gwamnan jihar Barno yayi wa ma’aikatan gwamnatin jihar ranar Juma’a, kashi 1 bisa 100 ne kawai ya iske a sakatariyan jihar.

Sabon gwamna Zulum ya garzaya sakatariyan jihar ne da misalin karfe 8:30 na safe. Gwamna Zulum yayi zauna har na tsawon awa daya a sakatariyan yana jiran ma’aikata su halarto amma shiru.

Ma’aikata 10 ne kacal ya samu a sakatariyan a lokacin da yayi wannan ziyara.

Zulum yace babban dalilin yin wannan ziyara kuwa shine koka masa da kungiyar kwadago na jihar tayi kan yadda ba ayi wa ma’aikatan adalci wajen biyan su albashin su da wasu hakkunan su akan kari.

Gwamnan ya gana da kungiyar kwadagon ne ranar Alhamis a fadar gwamnatin jihar.

Share.

game da Author