Makonni uku da sace Magajin Garin Daura har yanzu shiru

0

Magajin garin Daura Musa Umar ya yi makonni uku kenan yana tsare a hannun masu garkuwa da mutane kuma har yanzu din dai shiru babu wani bayani game da ceto sa.

Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Mayu ne masu garkuwa da mutane suka dauke Umar bayan ya dawo daga sallar magriba a kofar gidan sa.

Wasu da abin ya faru a idanunsu sun bayyanawa cewa masu garkuwan sun zo a mota kirar ‘Peugeot 406’ suka dauke shi da karfin tsiya suka tafi da shi.

Juyayin mazauna garin Daura

Mazaunan garin Daura da dama sun bayyana cewa har yanzu suna juyayin sace Umar da masu garkuwa suka yi.

Sun ce abin da ya fi ban mamaki shine yadda har yanzu babu labari a kansa.

” Ina tabbatar muku da cewa har yanzu mutanen garin Daura na juyayin abinda ya faru da basaraken. Ace wai ashigo har garin Daura a tafi da mutum kamar Magajin Gari sannan kuma abu kamar wasa tun ana jiya gashi har yanzu ya kai ga ana kirga makonni.” Inji Mamman Lawal.

Lawal yace har yanzu mutane na nan na kewansa saboda shi dama can mutum ne mai kowa nasa.

Shi kuwa Muhammed Abdullahi cewa yayi tuni har an dukufa da yin addu’o’i domin Allah ya fiddo da shi.

Da yake ganawa da PREMIUM TIMES jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike game da garkuwa da akayi da Magajin Gari. Sannan kuma har an yi nasarar kama wasu da ake zaton suna da hannu a wannan ta’asa.

” Ba za mu fadi irin kokarin da muke yi ba don ganin mun ceto Magajin Gari. Ian so ku sani ma cewa ana nan ana aiki kuma ma har mun yi kame da dama.

A taron raba irin auduga da ministan aiyukkan noma Audu Ogbe da gwamman babban bankin Najeriya Godwin Emiefele suka halarta a garin Katsina mai martaba sarkin Katsina Abdulmumini Usman ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukan mataki game da kashe-kashen da yaki ci yaki cinyewa a fadin jihar.

” Mahara sun addabe mu a jihar Katsina. A kullum sai kaji an far wa wani kauye a jihar. Saboda lalacewar abin ma har garin Daura a ka je aka yi garkuwa da Magajin Garin Daura. Manoma sun kaurace wa gonakinsu saboda ayyukan mahara da masu garkuwa.”

Sarki Usman ya ce babu wani alfanu raba irin noma ga manomin da ba zai iya zuwa gona yayi aiki ba.

” Ba Iri mutane ke nema ba, tsaro ne yafi damun mutane a jihar Katsina. Ku koma ku gaya wa Buhari halin da muke ciki a Katsina. Abin ya wuce fa gona da iri.

Saidai kuma a wannan mako Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta bada sanarwar kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane da suka wuce 70.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Sanusi Buba ne ya bayyana haka, a yayin da ya ke wa manema labarai bayanin nasarar da aka samu, tun bayan kafa ‘Operation Puff Adder’ a Jihar Katsina.

Ya ce daga cikin wadanda aka kama har da wanda ake zargi da yin garkuwa da surikar Gwamna Aminu Masari, mai suna Hauwa Yusuf.

An dai yi garkuwa da Hauwa a ranar 9 Ga Maris, 2019 bayan an je har cikin gidan ta an sace ta a cikin Katsina.

Buba ya ce an samu bindigogi kirar AK 47 har guda 43 a hannun wadanda ake zargi. An kuma samu motoci biyar, babura 44, bindigogin gargajiya guda 19, albarusai 1,500 da wasu kananan makamai.

Ya ce dukkan su sun amsa laifin su, kuma su na yi wa jami’an tsaro karin haske.

Wadanda aka kama da laifin sace surikar Masari sun hada da Abdullahi Sani, Abubakar Dani, Rabe Hamza, Gide da kuma Abdulkarim Bishir.

Ya ce ba da dadewa ba za a gurfanar da su kotu bayan kammala binciken su.

Idan ba a manta ba, an sace surikar Gwamna Masari har tsawon makonni biyu, inda aka sako ta bayan an biya diyyar naira milyan 30.

Share.

game da Author