Mahara sun yi garkuwa da dan sako a Zamfara

0

Mahara da suka bukaci sai an biya kudin fansa wato diyya har Naira miliyan 30 kan wani magidanci da suka yi garkuwa da shi sun yi garkuwa da dan sa.

Shi dai wannan magidanci ya fada hannun masu garkuwa da mutane ne misalin watanni biyu kenan.

Bayan tattaunawa da iyalai da ‘yan uwan wadannan mahara, sun ganganda sun tara naira miliyan 2.5 wa maharan.

” Da muka tara naira miliyan 2.5 sai muka aika musu da shi. Kanina ne muka ba kudin ya buga babur din sa ya tafi kai musu. Bayan ya iske su sai suka karbi kudin sannan suka kira mu cewa kudin yayi musu kadan shima kanin na wa ba zai dawo ba sun rike shi.

” Gaba daya duk wani abu da muke dashi mun tattara mun saida domin hada musu kudin. Gashi yanzu harda dan sakon ma sun rike shi wai baza su sako shi ba sai mun aika da miliyan 30.

” Yanzu dai mun zura wa sarautar Allah ido ne domin babu wani abu da za mu iya yi kuma.

A hankali a hankali dai ayyukan mahara da masu garkuwa da mutane ya samu gindin zama a wasu jihohi da dama domin haka kawai a duk lokacin da maharan suka dama sai su far wa kauye, su kashe na kashewa, su dauke na daukewa sannan su kwashi abinda suka ci karo da.

Share.

game da Author