Liverpool ta maida Barcelona gida cikin bakin ciki

0

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool da ke Ingila, sun yi wa Barcelona korar-kare daga gasar Champions League.

Wasn da suka buga yau da dare, an tashi 4:0 duk a kan Barcelona, duk kuwa da cewa a makon da ya gabata ta ci Liverpool kwallaye uku a Spain.

Tun a minti na 7 aka jefa wa Barcelona kwallo daya. Bayan an dawo hutu kuma aka sharara mata kwallaye uku a cikin raga.

Idan ba a manta ba, a Gasar 2007 da Liverpool ta ci kofin, sai da AC Milan ta Italiya ta sheka mata kwallaye uku, amma daga baya ta rama. Kuma ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Yanzu dai Liverpool na jiran wanda zai yi nasara a tsakanin Ajax da Tottenham.

Wannan ne karo na biyu a jere da Liverpool ta kai wasan karshe. Real Madrid ce ta hana ta cin Kofi a shekarar da ta gabata.

Ko za ta iya kai hannun ta a kofin a wannan ahekarar?

Share.

game da Author