Lauya ya nemi kotu ta dakatar da nadin da Buhari ya yi wa Emiefele

0

Wani lauya kuma kwararren dan busa usur din fallasa yadda ake satar kudade, mai suna George Uboh, ya kalubalanci kokarin da Gwamnatin Tarayya keyi na sake nada Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ci gaba da rike bankin karo na biyu.

Idan majalisa ta amince da tayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi mata na neman sake amincewar ta Emiefele ya rike shugabancin CBN, zai sake shafe wasu shekaru hudu kenan a matsayin sa na Gwamnan bankin.

Uboh wanda ejan ne na zakulo inda ake karkatar da kudade, ya nemi kotu kada ta amince a sake nada Emiefele shugabancin CBN.

A cikin dalilan da ya gabatar wa kotu, a takardar kara a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, Uboh yace wa kotu ba zai yiwu Gwamnatin Tarayya ta aika da sunan Godwin Emiefele wai Majalisar Dattawa ta sake amincewa da shi ba, domin akwai kara a gaban kotu, inda ake kalubalantar sake nada shi din.

Kwafin karar da Uboh ya shigar wanda ya fado a hannun PREMIUM TIMES, ya nuna ana zargin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emiefele ya hada baki da wasu shugabannin kamfanin NNPC sun damfari gwamnati da ’yan Najeriya.

Lauya Martin Okoye na JohnMary Jideobi ne ya shigar da karar, inda a ciki aka hada da kwafen rantsuwar cewa Emiefele ya hada baki da wasu shugabannin NNPC sun karkatar da dala milyan 24.

Ya ce an karkatar da kudin ne ta hanyar sayar da man fetur a Najeriya.

TONON SILILI

“Cikin watan Janairu, 2016, NNPC ta umarci CBN ya tura kudade har dala milyan 162, 064, 237.46 a asusun JP Morgan da ke CBN/JV mai lamba 001-1-658-366.

“An ce masa a cire kudin daga asusun NNPC da ke CBN, mai lamaba 400941775, wanda asusun kuma na tattara kudaden man fetur ne, wanda na ajiya ne ba na hada-hada ba ne.

“Bayan an cire kudin daga asusun tara ribar gas, sai kuma aka kafci dala milyan $24, 263, 008.56 daga asusun man fetur.

“Tunda dai dala milyan $162, 064, 237.46 ne NNPC ta ce a cire, sai aka cire dala milyan $186, 327, 246.02, hakan na nufin an yi awon-gaba da dala milyan $24, 263, 008.56 kenan, a matsayin ‘ribar-kafa.’

Lauyan duk kuma ya nuna wa kotu kwafen takardun shaidar yadda aka cire kudin, adadin da aka rubuta cewa a cire, da kuma yadda aka cire adadin da ya kamata a cire sannan aka dora sama da dala milyan 24 din a kai.

Zarge-zargen su na da yawa, amma dai a jimlace, Uboh ya ce Emiefele sun karkatar da kudade za su kai dala milyan 760.

Ya ce duk wadannan kudade an karkatar da su ne daga kudaden shigar da ke shigo wa Gwamnatin Tarayya daga man fetur din da ake sayarwa a kasashen ketare.

WANE NE GEAORGE UBOH?

George Uboh fitacce ne, a cikin 2016 gwamnatin tarayya ta ba shi aikin gano yadda wasu makudan kudade ke jibge a cikin wasu bankuna, wadanda an kasa gaba, kuma an kasa cirawa da su baya.

Bankunan da kudaden ke kimshe a lokacin sun hada da: Access Bank, First Bank, Zenith Bank, Diamond Bank, Fidelity Bank, UBA, Union Bank, Spring Bank-Enterprise Bank, Afribank-Mainstreet Bank, Oceanic Bank-Ecobank, Bank PHB-Keystone, FCMB da kuma WEMA Bank.

Bayan ya yi bincike da zakule-zakulen sa ya kammala, sai ya mika rahoton cewa akwai naira bilyan 47.14, dala milyan 598.7 da kuma fam milyan 23.5 kimshe a cikin wadannan bankuna guda goma.

KULLALLIYA?

Duk da wannan namijin kokari da George Uboh ya yi wa Gwamnatin Tarayya, maimakon a gode masa, sai Ministan Shari’a Abubakar Malami ya soke takardar yarjejeniyar daukar sa aiki da aka yi.

Ya soke yarjejeniyar ce tun a cikin watan Maris na shekarar da aka dauke shi aikin.

MAGANIN BIRI KAREN BAMAGUJE

Yanzu kuma George Uboh ya kwanto wa NNPC da Gwamnan Babban Bankin Najeriya kura.

Ya zarge su da yi wa makudan milyoyin daloli asarkala, wala-wala da rub-da-ciki.

Shin ko Majalisar Dokoki za ta amince ta sake yarda Shugaba Buhari ya sake bai wa Gwamnan CBN, Emiefele rikon amanar bankin karo na biyu?

Ko Buhari zai fasa sake daukar sa, sannan ya tsige shi kuma ya sa a bincike shi?

Ko Buhari zai sa abinciki shugabannin NNPC?

Shin ko duk za a hukunta su, idan aka same su da laifi?

Share.

game da Author