Kungiyar Kwadago ta nuna damuwa game da tulin bashin da ke kan Najeriya

0

Gamayyar Kungiyoyin Kwadago sun koka dangane da yawan tulin bashin da Najeriya ke ci gaba da ciwowa, kuma a kullum ya ke kara yawa.

Sun koka ne da yawan bashin da gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi ke ci gaba ciwowa a kasahsen waje.

Ta ce abin damuwa ne matuka ganinn yadda bashin da ke kan Najeriya wanda aka ciwo a kasashen waje ya karu matuka daga naira tirilyan 4.5 a cikin 2017 zuwa tirilyan 6.5 a cikin 2018.

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta Kasa, Ayuba Wabba ne ya nuna wannan damuwa a madadin daukacin ‘yan kungiyar.

Ya yi wannan bayani ne tare da Shugaban Kungiyoyin ‘Yan Kasuwa, wato TUC, Bobboi Kaigama, a wurin Bikin Murnar Ranar Ma’aikata, jiya Laraba, a Abuja.

Wabba ya kara da bayanin da Ofishin Kula Basussuka ya fitar, tun farkon makon jiya cewa:

“Ana bin Najeriya bashin sama da Naira tiriliyan 24. An ciwo naira tiriliyan 4.5 a cikin 2017, sannan kuma ya zuwa 2018 an ciwo tirilyan 6.5 ko kuma ya kai tirilyan 6.5.

“Kimanin kashi 2 bisa 3 na kudaden shigar da gwamnati ke samu, duk ana kashe su ne wajen biyan kudin ruwa na basussukan da aka karbo.

“Sannan kuma ana nan sa wa Najeriya ido cewa ta kokarta ta biya bashin nan da wa’adin da aka gindaya mata.

Wabba ya ce hatta “Babban Bankin Tarayya sai da kwanan nan ya ja hankalin Najeriya a kann yadda dimbin bashi ke ta hauhawa.”

Yayin da ya ke jawabi, Kaigama ya ce abin haushi da takaici shi ne yadda ‘yan Najeriya ba su ma cin moriyar ababen raya kasar da ake karbo bashin domin a samar da su.

Yayi korafin rashin wadatar hasken lantarki, ruwa, ilmi, kiwon lafiya da sauran su.

Share.

game da Author