Kungiyar Kwadago ta fara zanga-zangar game-gari

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta bada sanarwar barkewa da fara yajin aiki tun daga yau Litinin.

Yajin aikin ya bijiro ne sanadiyyar rikicin da kungiyar ke yi da Ministan Kwadago a kan shugabancin Hukumar Gudanarwar NSITF.

NLC da Ma’aikatar Kwadago kowa na goyon bayan wani bangare daban na Shugaban hukumar ta NSITF.

Jiya Lahadi NLC ta ce yanke hukuncin fara yajin aikin ya zama tilas, saboda matakin da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya dauka na da goyon baya da kuma sa hannun Shugaba Muhammdu Buhari.

Ta ce za a rantsar da hukumar gudamarwar NSITF yau Litnin a Abuja. Shi ya sa su kuma za su tsunduma yajin aki.

NLC ta ce su na mmakin yadda za a tura Frank Kokori ya tafi Cibiyar Horas da Ma’aikatan Kwadago a Ilorin, bayan daga farko shi ne aka tura shugabancin Hukumar Gudanarwar NISTF.

Kungiyar dai ta na goyon bayan Frank Kokori, yayin da a daya gefen kuma ta na zargin Minista Ngige ne ba ya goyon bayan sa, shi ya sa ya ki amincewa da nadin da aka yi masa tun da farko.

Idan ba a manta ba, cikin makon jiya ne ‘yan-takifen Ministan Kwadago Ngige suka doki ma’aikata masu zanga-zanga a kofar gidan Ngige a unguwar Asokoro.

Sun kuma yi wa wakiliyar PREMIUM TIMES ruwan duwatsu, suka kwace mata wayoyi biyu tare da sauran kayan da ke cikin jakar ta.

A yau NLC ta fara zanga-zanga tun da karfe 9 na safe daga Hedikwatar Kungiyar ta su ta kwadago, wato Labour House, a Abuja.

Shugaban NLC Ayuba Wabba ya shaida dalilin da ya sa suke zanga-zangar, kuma ya ce za a yi zanga-zanga a Majalisar Dinkin Duniya a ofishin da ke Genewa a ranar 18 Ga Mayu.

Share.

game da Author