Ku kunyata ministan kwadago Ngige a duk inda ku kayi ido hudu da shi– Kungiyar Kwadago

0

Kungiyar kwadago (NLC) ta yi kira ga mambobinta dake aiki a tashoshin jiragen sama da na kasa 163 da su kunyata ministan kwadago Chris Ngige a duk inda suka yi ido hudu da shi.

NLC ta yi wannan sanarwa ne bayan arangama da ta yi da wasu da ake zaton ‘yan jagaliyar Ngige ne suka far wa masu zanga-zanga.

Kungiyar kwadagon ta ce tana bukatan Ministan kwadago ya gaggauta bata hakuri bisa tarwatsa gangamin NLC a wajen Zanga-zanga.

Kungiyar ta fadi haka ne ranan Alhamis da yamma bayan fitowa daga ganawa da ta yi da mambobinta.

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba yace abin da ministan yayi nuni ne cewa bai cancanci ya ci gaba da zama a wannan kujera na minister ba.

” Ngige bai cancaci ci gaba da zama a matsayin ministan Kwadago ba domin shi yana ganin babu wanda ya-i-sa ya sashi ko ya hana shi. Saboda haka yanzu mun yi hannun riga da shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sunan Frank Kokori a matsayin shugaban hukumar NSITF wanda shi minista Ngige ya cire.

” Ngige ya cire sunan Kokori ne saboda ya san cewa Kokori ba mutumu ba ne da za a iya juya shi yadda ake so.

” Tun da Ngige yace ana cin hanci da rashawa a hukumar NSITF muna kira ga gwamnati da ta kafa kwamiti domin bankado wadanda suke aikata cin hanci da rashawa a hukumar.

Wabba yace zanga -zangar su a Abuja kawai suke yi, amma yana kira ga kungiyoyin kwadago dake jihohin kasar nan da su kwana da shiri domin za a kira gangami na duk kasa baki daya.

Minista Ngige

Ministan kwadago Chris Ngige ya ce zai shigar da kara kotu bisa muzguna masa da NLC ke yi.

” Kunyata mutum ba yana nufin ka je gidansa ba domin baka san wanda za ka taras ba a wurin.

” Abin da NLC ta yi ta’addanci ne ba aiyukkan kungiya ba domini kungiya tattaunawa da yarjejeniya ake yi da ita.

” Na yi mamakin yadda na ji cewa wasu na kwance a asibiti wasu har duka an yi musu a wajen Zanga-zangan. Lallai zan bincika in gani.

Ngige yace matsalar NLC shine rantsar da hukumar NSITF sannan bisa ga dokar ILO ministan kwadago ne ke da ikon bada sunayen wanda za a rantsar ba shugaban kasa ba ko mataimakinsa ko sakataren gwamnati ba.

Ma’aikatar Kwadago ta bada suna sannan gwamnati ta amince da sunan da ma’aikatar ta bada.

A dalilin haka gwamnati za ta rantsar da wadanda ma’aikatar kwadago ta amince da su.

Ngige yace tun farko bai bada sunan Frank Kokori ba.

Share.

game da Author