Babbar Kotun Jihar Jigawa ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum mai suna Datti Buba, saboda kama shi da aka yi da laifin yin garkuwa da kuma kashe wasu mutane biyu da ya yi a cikin jihar Jigawa.
Datti Buba wanda dan asalin garin Giade ne cikin Karamar Hukumar Bauchi, an same shi ne da laifin kashe wasu mutane biyu da yay i garkuwa da su.
Jihar Jigawa ce ta gurfanar da shi, inda aka tuhume shi da laifuka uku, da suka hada da haifin hada baki, garkuwa da mutane da kuma yi wasu mutane biyu kisan-gilla.
Mai Shari’a Ubale Ahmed ya zartas da hukuncin kisa a kan Buba ta hanyar ratayewa saboda kashe wasu mutane biyu da suka yi shi da wasu.
Ya furta wa mai shari’a da bakin sa cewa shi Adamu Sabo da Usman Idris, dukkan su ’yan Jihar Bauchi, sun aikata laifn garkuwa da kuma kisa kan mutane biyu a jihar Jigawa.
Sai dai kuma kotun ta wanke sauran wadanda Buba ya ce da su aka hada baki aka yi garkuwar.
Baya ga hukuncin kisa, an yanke masa shekara biyar a kan hada baki da kuma wasu shekaru goma na yin garkuwa da mutane.