Kotu ta warware nadin sabbin Sarakunan Kano hudu

0

Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta umarci Gwamna Abdullahi Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi cewa kowa ya tsaya matsayin sa, a kan umarcin da kotun ta bayar tun na ranar 10 Ga Mayu.

A waccan ranar dai kotun ta hana a nada sarakunan na Gaya, Bichi, Karaye da kuma Rano.

A yau kuma cikin wata sabuwar kara da wasu masu ikon nada sarki a Kano suka shigar, sun nemi kotu ta haramta nada sabbin sarakunan kuma ta hana kirkiro sabbin masarautun domin sun saba da ka’ida.

Mai Shari’a Sanusi ya ce a dakata tukunna har sai kotu ta yanke hukunci don haka nada sarakunan da kuma ba su sandunan girma duk haramtaccen nadi ne.

A wancan karo dai wani mai suna Rabiu Gwarzo ne ya garzaya kotu inda ya nemi a taka wa Gwamna Ganduje burki daga nada sarakunan da kuma kirkiro masarautun hudu.

Lauyan mai kara ya shaida wa kotu cewa wanda ake kara, wato Ganduje bai bi wancan umarci na kotu na farko ba.
Ya shaida wa kotu cewa an bada umarnin kada Ganduje ya yi nadin a ranar 13 Ga Mayu, shi kuma Ganduje ya nada su a ranar 14 Ga Mayu.

Sai dai kuma lauyan Gwamnati da Ganduje, wanda shi ne Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Muktar, ya ce ai batun nadin da kirkirar masarautun sun rigaya sun zama doka. Ya ce kotu ba ta da ikon warware nadin.

Hukuncin kotu na nufin cewa har yanzu Sarki Muhammadu Sanusi ll ya na nan a matsayin sa na Sarkin Kano gaba dayan kananan hukumin ta 44 ba.

Share.

game da Author