Kotun dake Igando a jihar Legas ta warware auren shekara 41 dake tsakanin Mabel Alli da mijin ta wanda fasto ne mai suna Richard saboda cin zarafin ‘ya’yan sa da ya haifa a gidan sa.
Ranar Alhamis alkalin kotun Adeniyi Koledoye yace warware auren dake tsakanin wadannan mutane ya zama dole ganin cewa ma’auratan sun gaji da zama tare.
” Daga yau na raba auren dake tsakanin Mabel da Richard.” Inji alkali.
Karar da Mabel ta shigar
A kwanakin baya Mabel mahaifiyar ‘ya’ya uku mata ta maka mijinta fasto Richard a kotu a dalilin dirkawa kanwarta ciki da ya yi.
Mabel ta bayyana cewa Richard ya hada ‘ya’yan su mata uku duk yana kwana da su.
” Akwai ranar dana kama miji na ido biyu yana kokarin danne babbar ‘yar mu mai shekaru 19 sannan har ya kai ga ya taba kai daya daga cikin ‘ya’yan mu asibiti a cire mata cikin da ya dirka mata.”
” Lalacewar Richard ya kai ga har ba zan iya daukan masu aiki mata ba sannan kanni na mata ma ba su iya kawo min ziyara saboda kafin a ankare ya danne yarin ya tunda nashi ma da ya haifa bai bar su ba.
Bayan haka ta ce Richard matsafi ne sannan sam baya kula da su iyalan sa.
Sai dai kuma shi Fasto Richard ya karyata duk wadannan zargi da matar sa ta bayyana a gaban alkali yana mai cewa ” Ni ba dan-iska bane, ban taba yin lalata da ‘ya’ya na ba ko kuma kawayen matata ba. duk wannan sharri ce kawai amma babu kanshin gaskiya a ciki.
” Sannan ni ba matsafi bane kamar yadda Mabel ke zargina da haka.
A karshe shima ya amince a raba auren kowa ya huta kawai tunda zargi ya shiga.