Babbar Kotun Jihar Kano ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje nada masarautu, har sai ta saurari karar da Gungun Mambobin Majalisar Dokokin Jihar ’yan jam’iyyar PDP suka kai gaban ta.
Jiya Juma’a ne mabobin jam’iyyar PDP a Majalisar Dokoki ta Jihar Kano suka garzaya kotu domin su hana Ganduje nadawa da kuma rantsar da sarakunan da ya nada a masarautu hudu da ya kara kafawa a lokacin da ya sa dokar daddatsa masarautar Kano.
Mambobin wadanda su ne marasa rinjaye, sun shigar da karar ca a bisa jagorancin Shugaban Masara Rinjaye, Rabiu Gwarzo, sun garzaya kotun domin neman a dakatar da Ganduje daga rantsar da nada sabbin sarakunan da ya yi niyyar yi a yau Juma’a, a bisa wasu dalilai biyar.
Sun bayyana wa kotu cewa ba a bi ka’idar da ya kamata a kira taron zama a zauren majalisa ba, kafin majalisa ta zartas da dokar karin masarautun guda hudu.
An yi zaman cikin gaggawa, kuma Gwamna Ganduje ya sa wa dokar hannu cikin gaggawa. Sannan kuma yay i gaggawar nada sakakunan, duk a cikin kwanaki biyu.
Sannan kuma a ranar Juma’a Ganduje ya shirya zai rantsar da su, kafin a shigar da karar taka masa burki.
Mai Shari’a Nasiru Saminu ya dakatar da Ganduje daga kirkiro Masrautun Gwarzo, Rano, Bichi da kuma Gaya.
Bayan ya bayar da sanarwar dakatar da Ganduje, mai shari’a ya sa ranar 15 Ga Mayu domin zama ranar fara zaman sauraren karar.
A hirar sa da PREMIUM TIMES, Hon. Gwarzo ya ce su ba su hana a yi wa Kano abin da ya dace a yi ba.
Sun ce amma ba za su yarda a yi mata abin da ba a bi kai’idar da doka ta gindaya ba.
Discussion about this post