Kotu dake Magajin Gari a Kaduna ta umarci ‘Yan sanda su tsare wata mata mai suna Karima Hama dake da shekaru 25 a dalilin kiran makwabciyar ta Jamila Sa’idu mai shekaru 26 Karuwa.
Alkalin kotun Musa Sa’ad -Goma ya yanke hukunci cewa ‘yan sanda su ci gaba da tsare Karima a ofishinsu har sai mijinta ya zo ya biya kudin belin ta.
Sa’ad-Goma ya dage shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Mayu.
Yayin da kotun ta zauna Jamila mazauniyar Hayin banki a Kaduna ta bayyana cewa Karima kan kira ta da munanan sunaye a duk lokacin da suka sami sabani.
” Karima kan kira ni da suna alade, karuwa a duk lokacin da fada ya hada mu. Da tura ta kai bango sai na kai karanta Wajen wanda ke kula da gidan hayan da muke ciki amma Karima bata daina jifa na da irin wadannan Kalamai ba.
” Ni ko da nan gaji da daukar irin wannan cin fuska shine na garzaya kotu domin karar ta.
Karima bata musanta haka a Kotu ba sai dai tace itama Jamilla tana yawan ce mata bata da hankali a duk lokacin da rikici ya kaure a tsakanin su.