A ranan Alhamis ne kotun majistare dake Ilori jihar Kwara ta daure wani magidanci mai suna Abdullahi Ali a kurkuku bisa zargin kashe mijin farkar sa da ya yi.
Alkalin kotun Malik Mogaji wanda ya yi kunnen uwar shegu da rokon sassauci da Ali ya nema yace Ali zai zauna a kurkukun Oke-Kura dake Ilori har sai an kammala bincike a hukumar gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Alkali Mogaji ya dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Yuni.
Lauyan da ya shigar da kara Adebayo Thomas ya bayyana a kotu cewa ‘yan sanda sun kama Ali ranar 26 ga watan Afrilu bayan ya kashe mijin farkarsa Salleh Zakariyau.
Thomas yace Ali da abokinsa Umaru suka shiga gidan Zakariyau dake karamar hukumar Bawagana Camp Via Baruteen suka kashe shi.
Ya ce bisa ga furicin da Ali ya yi a ofishin ‘yan sanda Ali yace ya kashe Zakariyau ne a dalilin gargadin da ya yi masa cewa ya fita harkar matarsa.
Discussion about this post