Kotu ta ce a gaggauta maida Shugaban SEC, Gwarzo a kan mulkin sa

0

Kotun Hukuncin Shari’un Masana’antu da Kamfanoni da ke Abuja, ta bada umarnin a gaggauta maida Shugaban Hukumar Kula da Hannayen Jari ta Kasa (SEC), Mounir Gwarzo a kan mukamin sa.

Mai Shari’a Sanusi Kado ya yanke hukuncin a yau Alhamis cewa ministar harkokin kudade ba ta da iko ko karfin ikon dakatar da Gwarzo da ta yi.

Kado ya yanke hukuncin cewa dakatar da Gwarzo da aka yi daga shugabancin SEC ba daidai ba ne, don haka ya maida shi a kan aikin sa da gaggawa.

Kado ya ci gaba da cewa maganar da ke gaban kotu kuwa ita kotu ta duba har ta yanke hukunci, it ace, shin wa ke da karfin ikon dakatar da Shugaban Hukumar SEC, ba shari’a ba ce a kan mukamin da ya ke a kai.

Mai Shari’a ya ce Shugaban SEC a karkashin Shugaban Kasa ya ke aiki, ba a karkashin Ministar Kudi ba, don haka shisshigi ne da karfa-karfa ta yi wa Gwarzo har ta dakatar da shi.

Ya ci gaba da cewa tabbas tunda babu hukumar gudanarwa, to Ministar Kudi na da nauyin aikin sa-ido a kan hukumar SEC, amma fa ba ta da karfin ikon da za ta iya hukunta shugaban hukumar, domin ba a karkashin ta ya ke ba.

Kado ya kara da cewa Babban Sakatare na Ma’aikatar Kudi ne kawai zai iya dakatar da Gwarzo, shi ma a bisa umarnin shugaban kasa, ba a bisa radin son ran sa ba.

Ya ce abin da kawai minista za ta iya yi shi ne ta rubuta takardar neman ‘a dakatar da shi kawai, amma ba ta dakatar da shi da kan ta ba.

Kado ya ce kwamitin da aka kafa ya dakatar da Gwarzo ai ba kotu ba ce; kuma ba kwamitin wasu alkalai ba ne da aka kafa su yi bincike.

Ya ce ya jingine sakamakon binciken da kwamiti ya yi a kan Gwarzo, don haka a gaggauta maida shi ya kammala wa’adin san a shekaru biyar.

Mai Shari’a Kado ya ce a biya Gwarzo dukkan kudaden albashin sa da aka rike da duk wasu alawus-alawus da suka wajaba ya rika karba idan ya na a kan mukamin sa.

Idan ba a manta ba, Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ce ta dakatar Gwazo a ranar 29 Ga Nuwamba, 2017.

Share.

game da Author