A hukuncin da kotun dake sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta yanke a yau Talata, Kotun bata amincewa jam’iyyar PDP ta yi binciken kwa-kwaf ba kamar yadda ta nema a gaban kotun.
Alkalin kotun maishahiri’a Halima Shamaki ta ce dokar zabe bata yarda da ayi wa takardun zabe binciken kwa-kwaf ba sai dai za a iya bin takardun da aka rubuta sakamakon zaben wanda aka yi fotokofi a dudduba.
Dama can lauyan dake kare jam’iyyar PDP Maliki Kuliya-Umar ne ya roki kotu da ta amince wa jam’iyyar ta yi irin wannan bincike.
Shi kuwa lauyan APC, Aliyu Umar ya ce bai dace kotu ta ba wani irin wannan dama ganin cewa hakan ya saba wa dokar hukumar Zabe da kasa.
Ita kanta hukumar Zabe ta ki amincewa da wannan dama da PDP ta nema a kotu.
Akarshe kotu ta ba jam’iyyar PDP din dama ta bincike takardun wadanda suke an riga an yi fotokofi din su domin ci gaba da shari’ar sannan su tsayar da lokacin da za agama dube-duben a dawo kan shari’ar tsangwararanta.