Shugaba Muhammadu Buhari ya na kan shan suka saboda nade-naden da ya yi na Shugabannin Fannonin Tsaro akasarin su duk ’yan Arewa ne.
An yi tunanin za su taka muhimmiyar rawa wajen dakile matsalar tsaro a kasar nan a shekaru hudu na farkon zangon Shugaba Buhari.
Shin ko cika ‘yan Arewa a akasarin mukaman shugabancin tsaro ya sa an samu saukin tsaro a kasar nan?
Kuma su wane ne wadannan shugabannin tukunna?
MINISTAN TSARO: Mansur Dan-Ali, dan Jihar Zamfara ne, jihar da ta fi kowace afkawa mummunar matsalar tsaro a cikin shekarun nan hudu.
BABBAN HAFSAN ASKARAWAN NAJERIYA: Tukur Buratai: Ya yi rawar ganin wajen karya fikafikin Boko Haram. Amma da ya ce sun gama da Boko Haram, shin an gama da su din ko kuwa har yanzu su na da barazana?
BABBAN HAFSAN SOJOJIN SAMA: Saddiqque Abubakar: Ko hare-haren da ake kaiwa ta sama sun kawo ci gaba sosai wajen dakile matsalar tsaro?
MASHAWARCIN SHUGABAN KASA A FANNIN TSARO: Babagana Monguno: Dan Jihar Barno ne. Wace shawara ya ke bayarwa da har za a iya cewa an ga aiki ya na kyau a yankuna irin Zamfara, Katsina, Kaduna da sauran wurare?
SHUGABAN HUKUMAR SHIGE DA FICE: Mohammed Babandede: Dan Jihar Jigawa ne: Ko an gamsu da yadda Hukumar Shige da Fice ke kula da yadda ke baki masu shigowa kasar nan barkatai? Ko sun iya sanin daga ina ake shigo da muggan makamai zuwa cikin kasar nan?
SHUGABAN HUKUMAR ‘YAN SANDA: Mohammed Adamu, kuma wanda ya sauka Adamu ya hau, wato Idris Ibrahim, shi ma dan Arewa ne: Shin aikin su ya yi kyau? Ya na yin kyau kuwa?
HUKUMAR DSS: Yusuf Magaji Bichi: Ya gaji Mathew Seiyefa, wanda ya yi ’yan watanni aka cire shi. amma kafin shi Lawan Daura ne ya fara yin zamani tare da Buhari.
MINISTAN HARKOKIN CIKIN GIDA: ABDUR-RAHMAN DAMBAZAU: Dan Kano ne. Shin ya aka yi harkokin tsaron cikin gida Najeriya ta lalace? Ya aka yi makamai ke shiga hannun ’yan bindiga? Daga ina ake shigo da su?
SHUGABAN HUKUMAR KWASTAN:Hamid Ali: Shin aikin sa na hana fasa-kwauri ya hana fasa-kwaurin muggan makamai zuwa cikin gida Najeriya kuwa? Ta yaya aka yi muggan bindigogi sun fi buhun shinkafa saukin samu a cikin wasu lunguna da kauyukan Arewa inda mahara ko ’yan binidiga suka yi babakere?
Karin Gishiri Ko Ribar-kafa: Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu da Shugaban Hukumar Kula Da Gidajen Kurkuku, Ja’afar Ahmed ma duk ’yan Arewa ne.