“Ina cikin jirgin Ehiopian Airline da ya kusa a fado a filin jirgin Saman Murtala Mohammaed dake Legas. Sai dai ban tada hankali na ba da jirgin ya ke tangal-tangal.”
Wannan sune kalaman Obasanjo da yayi wa PREMIUM TIMES bayan kuskure fadowa da jirgin da yake ciki yayi.
Tsohon shugaban Kasa Obasanjo ya halarci taro ne a kasar Ethipia inda jirgin da yake cike ya kusa fadowa wajen sauka a filin Murtala Mohammed dake Legas.
Obasanjo ya ce ko da jirgin ke tangan-tangal zaman sa yayi yana karatun jaridar sa. ” A haka ne wani da ke zaune kusa dani ya ce mini Oga, baka jin abinda yake faruwa ne? sai na ce masa ay babu abinda zan iyayi akai, a fa cikin jirgi muke. Na bar wa Allah komai.
Obasanjo ya ce daga nan sai ya ci gaba da karatun jaridar sa har Allah ya sa suka sauka Lafiya.
Direban Jirgin, ya bayyanawa fasinjojin dake cikin jigin su 390 cewa adaidai zai sauka sai ruwan sama da ake yi ya dan rikitar da shi daga nan ne ya ga idan yayi saukan farko zai iya shanye titin da zai tsaya bai tsaya sai ya sake tashi sama kafinnan ya dawo ya sauka.