Kotun majistare dake Ilorin jihar Kwara ta yake wa wani makiyayi da aka zarga da kisan kai hukuncin zama a kurkukun Oke -Kura har sai ta kammala sauraren karan.
Lauyan da ya shigar da karan Abegunde Elijah ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama Sulaiman Adamu da laifin kisa ne bayan karan da danuwan mamacin ya shigar.
Elijah ya ce ‘yan sandan sun gano bindigogi biyu, harsasai shida da takalmin roba daya a gidan Adamu.
Ya kuma ce bincike ya nuna cewa Adamu ya kashe wani mazaunin Dutsi Camp dake karamar hukumar Moro a jihar mai suna Abdulkareem Musa.
Alkalin kotun Mariam Yahaya ta yi watsi da rokon sassauci da Adamu ya yi sannan ta daga shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Mayu domin yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka dake Kwara.