Shugabar Kotun Daukaka Kara ta kasa, Zainab Bulkachuwa, ta cire kan ta daga shugabanci ko zama mamba ta Kotun Daukaka Karar Shugaban Kasa.
An kafa kotun mai alkalai shida domin sauraren kararrakin zaben shugaban kasa wanda Atiku Abubakar da PDP da kuma wasu jam’iyyu hudu suka gurfanar da Shugaba Muhammadu Buhari, APC da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Hakan ya biyo bayan karar da Atiku Abubakar ya shigar cewa bai yarda da Zainab Bulkachuwa ta kasance cikin masu shari’ar karar da ya kai Buhari da APC ba.
Atiku ya kafa hujjar cewa Zainab na da alaka da jam’iyyyar APC ta kut da kut, domin mijin ta Mohammed Bulkachuwa babban jigo ne a jam’iyyar APC, kuma ya ci kujerar sanatan APC daga jihar Bauchi.
Baya ga wannan kuma, Atiku da PDP sun ce akwai daya daga cikin ‘ya’yan Zainab Bulkachuwa da ya yi takarar zaben fidda gwani a jam’iyyar APC, amma bai yi nasara ba.
Har ila yau, Atiku ya ce dan na Zainab ya rika taya Shugaba Muhammadu Buhari kamfen, a shafin sa na soshiyar midiya, wato Facebook, inda a can din ma ya rika tallata katarar sa ta neman gwamnan a karkashin APC.
Akan haka ne Atiku ya ce bai ga yadda za a yi kotun ta yi masa adalci ba, muddin Zainab ce shugagan alkalan ko kuma ta na cikin mambobin da za yi alkalancin.
Bulkachuwa ta bayyana janyewar ce a yau Laraba, duk kuwa da cewa alkalan da za su fara sauraren shari’ar sun nuna kin amincewar ta janye din.