Mutanen karamar hukumar Wudil dake jihar Kano sun yi kira da kakkausar murya ga gwamnatin jihar Kano da ta sani cewa ba za ta hade da masarautar Gaya ba kamar yadda ya nuna a sabbin masarautun ga aka kirkiro.
Shugaban kungiyar, Yawale Idris ya sanar da haka a taron ‘yan jarida a Kano.
” Babu wanda ya tuntube mu kafin a aiwatar da wannan sabon abu. Mu mutanen Wudil ba tare muke da Gaya ba, saboda haka dole a koma kan teburin shawara a maido da yadda tsarin yake tuntuni domin ba zamu yarda a sakalamu a wani masarauta da bamu da alaka ko tarihi da su ba.
Idris yace tabbas ida har aka yi haka to kiri-kiri ana shafe tarihin su ne a doron kasa.
” Muna da asalin mu kuma muna da cikakken tarihin mutanen mu. Mu Jobawa ne wanda daya ne daga cikin gidajen sarautar Kano da ke da Tuta saboda haka muna so gwamnan Kano ya sani. Sannan kuma muna so ya sani cewa dukkan mutanen Mudil mun yi mubaya a ne ga sarkin Kano Sanusi da masarautar Kano ba za mu bi masarautar Gaya ba.
” Tun a lokacin jihadin Usman Danfodio gidajen fulani biyar ne aka basu tuta a Kano wadanna gidaje kuwa sune, Sullubawa (wanda shine gidan su Sarki Sanusi mai mulki), Jobawa ( Masu sarautar Wudil), Yolawa (Masu sarautar Dawakin Tofa), Danbazawa (Masu sarautar Dambatta) da Gyanawa ( Masu sarautar Gabasawa).
A yau Asabar ne ake sauraron saukar jirgin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a filin jirgin Aminu kano bayan tafiya da yayi kasar Ingila.
Dubban magoya bayan sarki Sanusi da mutanen Kano ne suka yi tattaki zuwa filin jirgin saman domin jiran saukan jirgin sarki Sanusi.
Wasu da suka zanta da wakilin mu a Kano sun ce garin ya rincabe, masoyan sarki Sanusi sun fito kwansu da kwarkwata domin yi wa sarkin Lale-marhaban.
Ana sa ran jirgin Sarki zai sauka ne da misalin Karfe 4 na yamma a filin jirgi na Aminu Kano.
Har yanzu dai sarkin Kano Sanusi bai ce uffan ba game da daddatsa masarautar Kano da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje yayi.
Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya fasa masarautar Kano inda ya kirkiro sabbin masarautu har guda hudu.
Mutane da dama sun yi tir da wannan masarautu da Ganduje ya kirkiru suna masu cewa yana yi wa sarki bita da kulli ne kawai don siyasa ba wai don yaga hakan ya cancanta a yi ba ko kuma daukakar jihar Kano.
Cikin kwana uku kacal, majalisar jihar Kano karanta wannan kudiri da wani dan majalisa ya mika a gabanta. A rana ta karshe kuwa wato cikon na ukun, Kakakin Majalisa da wasu daga cikin wakilan majalisar suka garzaya fadar gwamnati inda nan take gwamna Ganduje bai yi wata-wata ba rattaba hannau a wannan kudiri ta zama doka.
Masarautun da gabduje ya kirkiro sun hada da Masarautar Karaye, Masarautar Rano, Masarautar Bichi da masarautar Gaya.