Kananan hukumomi 11 a Najeriya basu yin bahaya a waje – UNICEF

0

Sakamakon binciken da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) da kungiyar tsaftace jiki da muhalli (WASH) ya nuna cewa kananan hukumomi 11 basa yin bahaya a waje a Najeriya.

Jami’in UNICEF da WASH Bioye Ogunjobi ya bayyana haka ne a taron wayar da kan mutane kan mahimmancin tsaftace muhalli da ilollin yin bahaya a waje da aka yi a Abuja.

Kananan hukumoni sun hada da Daas da Warji a jihar Bauchi; Birnin Kudu da Buji a jihar Jigawa; Ikom, Yala, Obanliku, Yakur, Boki da Berkwara a jihar Cross Rivers da Logo a jihar Benuwai.

UNICEF da WASH sunce akwai yiwuwar samun karin kananan hukumomi biyu daga jihar Jigawa.

Ogunjobi yace kananan hukumomin sun yi nasarar tsaftace muhallinsu ta hanyar hana yin bahaya a waje a dalilin goyan bayan da suka samu daga wajen ma’aikatar ruwa, UNICEF da WASH da kuma shirin nan na‘Community Led Total Sanitation (CLT)’ ta suka kirkiro.

‘‘CLT shiri ne dake taimakawa wajen karkato da hankulan mutanen musamman mazauna karkara game da illolin dake tattare da rashin wadata dakunan bahaya da tsaftace muhalli.

Hakan ya nuna cewa akwai sauran aiki a a gaban gwamnati musamman idan tana bukatan cimma wannan buri nata na tabbatar da samun tsaftataccen muhalli zuwa shekarar 2025.

Jami’in ma’aikatar yada labarai Olumide Osanyinpeju ya yi kira ga gidajen jaridu kan hada hannu da yaki da rashin tsaftace muhalli da suka yi wa taken ‘Tsaftattaciyyar Najeriya: Yi amfani da ban daki’ domin wayar da kan mutane kan mahimmancin tsaftace muhalli da sannan
karkato da hankulan gwamnatoci wajen samar da manufofin da za su taimaka wajen ganin an samu nasara akan haka.

Share.

game da Author