Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa har yanzu akwai jihohi 14 a kasar nan da basu karbi kudin tallafin kiwon lafiya na ‘Basic Health Care Provision Fund (BHCPF)’ ba.
Adewole ya fadi haka ne ranar Talata a zauren majalisar dattawa inda ya kara da cewa jihohi 22 ne suke karban wannan tallafi.
Ya ce rashin nuna ra’ayin karban tallafin da rashin cika sharuddan samun tallafin na daga cikin dalilan da ya hana wadannan jihohin samun tallafin.
” Sharuddan samun tallafin sun hada da kafa hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, Kafa inshoran kiwon lafiya na jihar da bada gudunmawar Naira biliyan 100.
Ga jerin jihohin
1. Kebbi
2. Jigawa
3. Akwa Ibom
4. Cross River
5. Gombe
6. Rivers
7. Borno
8. Zamfara.
9. Ondo
10. Benue
11. Taraba
12. Nasarawa
13. Ogun
14. Sokoto.
Discussion about this post