JIHAR KATSINA: Mahara sun kashe ‘yan sintiri biyar –Inji ‘yan sanda

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da kisan ‘yan sintiri biyar da mahara suka yi.

Sanarwar daga jami’an tsaro ta ce an kashe masu sintiri na bijilante ne su biyar a Karamar Hukumar Faskari.

Faskari ta yi iyaka da Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina da kuma Tsafe a Jihar Zamfara, yankunan da hare-hare da garkuwa da mutane suka yi muni sosai.

Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Katsina, Gambo Isa, ya ce an kashe masu sintirin ne a kauyen Sabon Layi da ke cikin Karamar Hukumar Faskari.

Masu sintirin da aka fi sani da ’yan sa-kai, sun yi gangancin shiga cikin daji domin su yi artabu da masu garkuwa da jama’a.

Ya ce an maharan sun kashe ‘yan sa-kai din ne a lokacin da suka bude masu wuta.

DPO na Karamar Hukumar ne ya ja ayarin jami’an tsaro suka kwaso gawarwakin masu sintirin, kuma suka gano wani sansani ko kuma mabuyar ’yan bindigar da suka gudu suka bari.

Share.

game da Author