JAMHURIYAR NIJAR: Tanka dauke da fetur ta yi bindiga, ta kashe mutane 55

0

Wata tankar mota dauke da mai ta fashe, ta yi bindiga, inda nan take ta kashe mutene 55.

Al’amarin ya faru ne yau Litinin a Yamai, babban birnin Jmahuriyar Nijar.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Nijar, Mohammed Bazzoum ne ya fitar da sanarwar.

Tankar wadda ke dauke da mai ta yi bindiga ne a lokacin da jama’a suka yi dandazo sun a kwasar man fetur din da ya zube daga cikin motar.
Haka dai Minista Bazzoum ya sanar a shafin sa na twitter.

Sanarwar ta kuma kara da cewa wasu mutane 37 da suka ji ciwo kuma a yanzu haka su na asibiti a birnin Yamai.

Share.

game da Author