Isa Ashiru ya bukaci kotu ta basu dama a sake kirga kuri’un zaben gwamnan jihar Kaduna

0

Kotun dake sauraren kararrakin zabe dake zama a Kaduna ta saurari karar da Lauyan jam’iyyar PDP ya shigar ya na neman a basu dama su sake kirga kuri’un da aka kada a zaben gwamnan jihar Kaduna.

Lauyan Ashiru, Elisha Kurah ya bayyanawa kotu cewa lallai suna bukatan kotu ta amince a sake kirga zaben gwamna na Kaduna da aka bayyana Nasir El-Rufai a matsayin wanda yayi nasara.

Alkalin Kotun I M Bako ya dage shari’ar zuwa ranar 25 ga watan mayu domin aba hukumar zabe da lauyan gwamna El-Rufai da su kare kan su game da wannan dama da PDP ke nema.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman Kotun, Lauyan PDP, Kura ya ce sun mika a gaban kotu ta bada wannan dama a sake kirga kuriun da aka kada a zaben gwamna na Kaduna.

” Yin haka na da matukar muhimmanci domin kuwa muna da sahihan hujjoji a kasa cewa mafi yawa daga cikin sakamakon da aka bayyana duk na boge ne.

” Kusan duka sakamakon rubutawa aka yi kawai ba ainihin abin da mutane suka zaba bane.Ina tabbatar muku da cewa idan har aka sake kirgen dalla-dalla PDP ce zata yi nasara ba APC ba. Amma kawai Kuri’u ne aka rika daddankarawa a takardar zabe wanda ba su kuma babu dalilin su kawai don APC ta yi nasara.

A nashi tsokacin, Lauyan gwamna El-Rufai, Abdulhakeem Mustapha ya musanta hakan, yana mai cewa bai ga yadda za a ce za a sake kirga kuri’u ba a bainar jama’a dalla-dalla. ” Wannan Ihu ne bayan hari PDP da dan takaranta Isah Ashiru ke yi.”

” Gaba daya bamu yarda da korafe-korafen da suka mika a gaban kotu ba. Baza mu yarda da su ba. Jama’an jihar Kaduna sun zabi wanda suke so kuma sun zabi Nasir El-Rufai ne.

Share.

game da Author