Jami’in hukumar kula da aiyukkan masu sarrafa magungunan gargajiyya reshen jihar Legas Kadiku Olorunkemi ya bayyana cewa gwamnati za ta iya cimma burinta na samar da kiwon lafiya mai nagarta ga kowa da kowa a kasarnan idan ta hada hannu da sashen magungunan gargajiya.
Olorunkemi ya fadi haka ne da ya ke amsar bakuncin mambobin ‘yan kungiyar NIPSS a Legas.
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta gane cewa mutane yanzu sun karkata zuwa ga amfani da magungunan gargajiya saboda tsadar da magungunan zamani ke da shi.
” Kafin kimiya ta gano maganin bature da maganin gargajiya muke amfani wajen warkar da cututtuka.
” Sai gashi yau an wayi gari maganin zamani ya nuna ya fi magungunan gargajiya inganci wanda hakan ba gaskiya bane domin bincike ya nuna cewa akan kamu da munanan cututtuka ta hanyar shan magungunan bature.
Bunkasa Asusun Kasa
Olorunkemi ya bayyana cewa magungunan gargajiyya na da karfin bunkasa asusun kasa idan gwamnati da masu fada a ji sun yi wa fannin tanadi.
Ya ce a yanzu haka kasashen Sin da India na amfani da magungunan gargajiya a fannin kiwon lafiyar su sannan hakan ya kai ga har fitar da magungunan zuwa kasashen waje ake yi saboda ingancin da suke da shi.
Olorunkemi yace tanada kudade domin gudanar da bincike a fannin magungunan gargajiya na cikin hanyoyin da za su taimaka wajen bunkasa kiwon lafiyar mutane da asusun kasa.
Matsalolin da fannin magungunan gargajiyya ke fama da su
Jagoran tawagar NIPSS Nasirudeen Usman ya ce rashin sanin yadda za a rika shan maganin gargajiya, rashin nuna yadda ake hada magungunan, rashin yi wa magungunan gargajiya rajista da hukumomin da suka kamata na dga cikin matsalolin dake hana magungunan samun karbuwa.
” Tabas maganin gargajiya na da matukar amfani musamma a fannin inganta kiwon lafiyar mutum sai dai rashin kafa hukumar da za ta dauki nauyin duba aiyukkan da masu sarrafa magungunan ke yi a kasar nan na daga cikin matsalolin dake hana maganin karbuwa.
Amma maganin gargajiyya magunguna ne da za sau taimaka wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasarnan ganin cewa maganin na da inganci da saukin farashi.
Matakan kawar da matsalolin da magunguna gargajiyya ke fama da su
Olorunkemi ya ce domin kawar da baragurbin masu sarrafa jabun magungunan gargajiyya gwamnatin jihar Legas ta kafa hukumar kula da aiyukkan sarrafa magungunan gargajiyya.
A yanzu haka hukumar ta kama masu sarrafa jabun magungunan gargajiyya da dama a jihar wanda bayan gudanar da bincike za a kai su kotu.
Olorunkemi yace hukumar za ta kama duk mai sarrafa maganin da bai yi rajista da hukumar ba tare da bayyana yadda suka hada magungunan su.