INEC ta janye shaidar zaben Kawu Sumaila, ta damka wa dan Minista Dambazau

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta damka satifiket na shaidar nasarar zaben da Mai Taimakawa Na Musamman Ga Shugaban Kasa Sulaiman Kawu-Sumaila ya ke rike dashi a da, ta damka wa dan Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurrahman Dmabazau.

Da farko kotun INEC ta damka shaidar ce ga Kawu Sumaila, wanda ya taba yin wakilin tarayya na Takai/Sumaila har sau uku, wanda kuma shi ne ya yi zabe a 2019.

Amma kuma sai Babbar Kotun Tarayya ta Kano, a ranar 18 Ga Afrilu, ta soke takarar Kawu, bisa dalilin kotun cewa ba bisa ka’ida ya fito takara ba.

Shamsudden Dambazau ya garzaya kotu inda ya kalubalanci Kawu Sumaila a matsayin dan takarar APC, a bisa dalilin cewa Sumaila bai tsaya takara a zaben fidda gwanin APC na dan majalisar tarayyar Takai/Sumaila ba.

Amina Zakari, wadda Kwamishinar Zabe ta Kasa ce, ta damka wa Shamsuddeen Dambazau shaidar a ranar Litinin.

Da ta ke damka masa shaidar, Amina ta ce INEC ta na bin umarnin kotu ne.

Da farko Kawu Sumaila ya fito takarar Sanata ne, amma sai Kabiru Gaya ya kayar da shi a zaben fidda-gwani. An ba shi yakarar Dan Majalisar Tarayya na Takai/Sumaila, mukamin da ya taba yi har sau uku a baya.

Shamsuddeen Dambazau ya kai kara a bisa dalilin cewa bai tsaya takarar zaben fidda-gwani ba.

Share.

game da Author