INEC ta fara bin-diddigin yadda zaben 2019 ya gudana

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta fara nazari da bin-diddigin hanyoyin da ta bi ta gudanar da zaben 2019.

A cikin wani bayani daga bakin Farfesa Mahmood Yakubu da INEC ta fitar, shugaban na INEC ya ce a cikin watanni biyu masu zuwa za ta yi amfani da masu ruwa da tsaki dangane jin ta bakin su wajen abubuwan da suka faru yayin zaben.

Sannan kuma za a ji ra’ayoyin jama’a a fadin kasar nan.

Yakubu ya bayyana haka a lokacin da ya ke gudanar da taro tare Kwamishinonin Hukumar Zabe gaba dayan su a Hedikwatar INEC, a Abuja.

Ya ce za a fara ne da jami’an INEC da kuma ma’aikatan wucin-gadi da INEC ta dauka aiki a lokacin zabe.

Daga nan kamar yadda Yakubu ya kara yin bayani, hukumar za kuma ta rika yin tarukan tuntubar juna da jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, kungiyoyin rajin kare dimokradiyya, kafafen yada labarai, masu sa-ido, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai.

Farfesa Mahmood Yakubu ya kara da cewa a wannan bin-diddigin za a gudanar, INEC za ta yi la’akari da rahotannin kwamitocin gyaran dokokin zabe da aka taba kafawa a baya.

Sannan kuma za ta yi la’akari da hukunce-hukuncen da kotunan daukaka kararrakin zabe suka yanke da kuma shawarwarin da aka taba bayarwa a baya.

“Tuni wasu masu aikin sa-ido sun gabatar da nasu shawarwari ko kuma tsokaci da rahotanni dangane da zabukan na 2019. Sannan kuma wasu kungiyoyin sa-kai na rajin dimokradiyya da dama sun yaba wa INEC a kan kokarin da ta yi.” Cewar Yakubu.

Share.

game da Author