Illoli 10 da shan ruwan sanyi ke haddasawa

0

A wannan lokaci da ake fama da zafi mutane da dama kan bukaci shan ruwa mai sanyi,ko a sha wasu abUbuwa masu sanyi ko kuma a zauna a wuri mai sanyi domin rage zafin da ake ji a jiki.

Duk da cewa yin haka kan taimaka wajen rage zafi amma malaman asibiti sun bayyana cewa yawaita yin haka na matukar cutar da kiwon lafiyar mutum.

Malaman asibiti sun bayyana cewa yawaita shan ruwa mai sanyi ko kuma zama a wuri mai sanyi kan sa a kamu da cutar hakarkari wato ‘pneumonia’ da turanci, Sanyin kashi, toshewar murya, mura da dai sauran su.

Domin guje wa kamuwa da wadannan matsalolin kamata ya yi a rage yawan shan ruwan sanyi da zama a wuri mai sanyi.

Ga wasu matsalolin da shan ruwan sanyi da yawan zama a wuri mai sanyi ke kawowa.

1. Akan kamu da mura.

2. Akan kamu da sanyin kashi.

3. Sanyi kan toshe wa mutum murya da haddasa cutrar makogoro wato ‘sorethroat’ a turance.

4. Akan haifi yaran dake dauke da cutar hakarkari wato ‘Pneumonia’ da turanci.

5. Yawan shan ruwan sanyi na rage karfin mazakutan namiji sannan ya hana mace haihuwa.

6. Yana kawo ciwon koda.

7. Yana hadasa ciwon kai ‘Migraine’

8. Shan ruwan sanyi na saurin busar da ruwan jikin mutum illa ya kara sa mutun jin kishin ruwa.

9. Yana lalata tsarin hanjin cikin mutum inda haka ke hana abinci narkewa a ciki.

10. Yana rage karfin jiki.

Share.

game da Author