Idan Najeriya ba ta ciwo bashi a Chana ba, ina za ta ciwo shi? -Amaechi

0

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Najeriya ba ta bai wa kasar Chana jinginar manyar kadarori kamar tashoshin jiragen ruwa ba, kafin ta ciwo bashi daga kasar.

Amaechi ya yi wannan jawabi ne a taron Harkokin Sufuri na Afrika ta Gabas da aka gudanar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Wannan karin bayani ya biyo bayan damuwar da aka ta yi cewa kasashen Sri Lanka, Sudan, Somalia da Kenya sai da suka bada jinginar tashoshin jiragen ruwa kafin Chana ta dibga musu basussukan da suka kasa biya.

Ana watsa cewa kasar Chana na shirye-shiryen karbe tashoshin na su, saboda kasa biyan basussukan da suka ci.

Amaechi ya ce babu wata sarkakiya tsakanin Najeriya da Chana, domin bashin da Najeriya ta ciwo ba mai wahalar biya ba ne. Sannan kuma babu yarjejeniyar damka musu kadara a matsayin jingina kafin mu karbi bashin.

Ya kuma nuna cewa basussukan da wasu kasashe suka ci, suka kasa biya a Chana, ya na shafar kikarin da Najeriya ke yi idan ta je bidar bashi a Chana.

“Dalilin da ya sa mu ke karakainar zuwa Chana, saboda ita kadai ce kasar da za ta bada bashi ga kasa domin gina abubuwan inganta rayuwar jama’a.

Ya ce su kan.su kasashen da suka ci gaba su na zuwa Chana su ciwo bashi.

” Idan ba ka je Chana ka ciwo bashi ba, a ina za ka je a ba ka? Hatta Amurka da Rasha duo su na zuwa Chana su ciwo bashi. To mene ne aibi don Najeriya ta ciwo bashi a Chana?” Inji Amaechi.

“Matsalar da mu ke fuskanta a Najeriya ita ce, fasinja ne kadai ke shiga jiragen kasa da mu ke samarwa a yanzu. To kuma ba a samun ribar ko sisi da kudin tikitin fasinja.

“Ba za mu fara samun riba ba, har sai an daina jigilar kaya masu nauyi ko masu yawa a mota, an dawo ana yi a jiragen kasa.

” To matsalar kenan, masu kaya sun ki rika loda kayan su a jiragen kasa, sai a mota. Kuma wadannan kayan su ke kashe mana titina, saboda kayan nauyi ne.” Inji Amaechi.

Share.

game da Author