IDAN KUNNE YA JI: Hanyoyin rabuwa lafiya da dan sandan Najeriya

0

Jiya Litinin ne Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bada sanarwar hanyoyin da suka kamata ko suka wajaba jama’a su rika nuna ladabi wajen shingen binciken motoci a kan titi.

An bayyana wannan sanarwa ce a shafin rundunar na tiwita.

An bijiro da wadannan shawarwarin ne sakamakon yadda ake samun yawaitar kashe fararen hula da jami’an ‘yan sanda ke yi a kasar nan.

Dama a ranar 17 Ga Afrilu, Jami’in Hulda da Jama’a Yemi Shogunde, ya shiga shafin sa na twitter, ya rubuta cewa, “Idan ka hadu da dan sanda, to ka daina yi masa Turancin Ingila, mai kama da Turancin Sarauniya. Kawai ka yi masa Turancin gargajiga, wato ‘pidgin’.

*Kada ka tsaya ka na sa-in-sa ko gadandami da dan sanda ko rigima da shi idan ya na kan aikin sa.

*Ka daina murtuke fuska, ka na nuna bacin-rai idan ka hadu da sanda a shingen binciken motoci, wato ‘check points’.

Ya ce idan ka bi wadannan shawarwarin, to hakan zai taimaka wajen saukin fahimtar juna tsakanin ka da dan sandan Najeriya.

HANYOYIN RABUWA LAFIYA DA DAN SANDAN NAJERIYA

1. Ka rage gudu idan ka tunkaro shigen binciken motoci. Hakan zai nuna cewa ba ka tukin-ganganci. Kuma idan ka rage gudu, ba za a yi zargin kai mai laifi ba ne, wanda zai taka mota ya zura a guje.

2. Da ka kusa wurin ‘yan sanda, to ka rage karar radiyon motar ka. Yin haka nuna da’a ce da mutunci. Kuma ka ga kai da dan sanda kowa zai ji abin da kowa ke fadi. Idan ka yin haka, dan sanda ba zai yi maka wani zargi nan da nan ba.

3. Ka fito da hannayen ka, kada ka boye su a cikin wani wurin da dan sanda zai yi zargin ka na kokarin dauko bindiga ce ko wani makamin da za ka lahanta shi.

4. Ka kunna wutar fitilar cikin motar ka, idan da dare ne. hakan ya na nuna wad an sanda cewa ba ka boye komai a cikin motar ka ba.

5. Ka bi su da lalama, cikin sanyin rai da kuma fara’a. Ka iya jinjina musu, ka yaba musu, musamman idan ka ga su na aiki a cikin rana, ko lokacin sanyi, ko ana sheka ruwa.

Ka tuna, idan ka yi wa mudubi murmushi, shi ma na cikin mudubin murmushi zai yi maka.

6. Ka yi kokari ka rika amsa duk wata tambayar da za su yi maka a cikin sanyin rai da ladabi.

7. Kada ka kuskura ka yi fada ko sa-in-sa da dan sandan da ke rike da bindiga. Wani lokaci za ka ji mutum na ce wa dan sanda, “ka harbe ni mana idan ka isa!” To ka sani fa yin haka kira wa kai bala’i ne. Ehe!

Saboda ba ka san ko a cikin wane hali ko yanayi dan sandan ya ke ba.

8. Kada ka kuskura ka yi kokawa da sanda dauke da bindiga. Zai yi tunanin yin amfani da bindigar sa ya kare kan sa, ko da shi ko kai ke da gaskiya.

9. Babu ruwan ka da sa-in-sa da dan sanda ko gardandami da shi. Akwai hanyoyin da za ka bi sun fi dubu wadanda za ka nemi hakki idan har an ci zarafin ka.

10. Kada ka kuskura ka taba dan sanda, musamman a cikin fushi. Zai yi tunanin kokari ka ke ka kwace bindigar sa.

11. Idan ka kasance ka na yawan bin wata hanya ce inda ’yan sanda ke tsayawa, to ka yi kokarin samun lambar da ‘yan sanda suka ce mutanen yankin su rika kira idan wani lamari na gaggawa ya taso.

12. A koda yaushe ka kasance takardun motar ka a kammale suke, kuma kada ka rika yin wasu halaye na karya dokokin tuki.

13. Kada ka rika nuna irin halin nan wai kai ba ka ma kaunar ganin dan sanda a kan hanya wurin aikin sa. Kada kuma ya fizgi mota a guje a lokacin da ake binciken ka. Ehe!

14. Idan ka tsaya ka ga dan sanda na yi maka wani abin da bai dace ba, to ka yi kokarin daukar sunan sa, ko lamabar kakin sa, ko lambar bindigar sa ko lambar motar su.

15. Idan ka zo shingen kan titi, har abu na neman kwabe maka kai da su, to ka nemi magana da babban su kai tsaye, a cikin murya mai sanyi.

16. Ka bi su a hankali, kuma idan ka ga ba a yi maka abin da ya kamata ba, to ka nuna musu sai dai a tafi ofishin su kai-tsaye kawai.

Share.

game da Author