HUKUNCIN KOTUN KOLI: Yari, Mukhtar sun sha kasa, za a biya Marafa miliyan 10

0

Kotun Koli ta ce duka kuri’un da aka kada wa jam’iyyar APC a Zamfara kuri’un banza ne, basu da amfani.

Kotun ta bayyana haka ne a hukuncin da ta yanke a yau.

Alkalan kotun biyar sun ce tabbas APC ba ta yi zaben fidda gwani a jihar Zamfara ba saboda haka jam’iyyar da ta zo na biyu ne sannan ta cika sharuddan zabe za a rantsar ranar 29 ga wata.

Yanzu dai murna ya koma ciki ga duk zababbun ‘yan takarar APC a jihar Zamfara domin kowa zai tattara nashi-shi-ina-shi ya kara gaba.

Wadanda suka zo na biyu ne za a rantsar a ranar 29 ga wata. Sannan bayan haka jam’iyyar za ta biya sanata Kabiru Marafa zunzurutun kudi har Naira miliyan 10 a dalilin kada ita da yayi a kotun koli.

Share.

game da Author