Hukumar Zabe ta dage zaben Kogi da Bayelsa

0

Hukumar zabe ta sanar da jirkita ranakun zaben gwamna na jihohin Kogi da Bayelsa.

Darektan wayar da kan mutane game da harkokin zabe na hukumar Festus Okoye ne ya bayyana haka ranar Alhamis.

Okoye ya ce hukumar ta yanke wannan shawara ne bayan ta saurari kukan gwamnati da mutanen jihar Bayelsa na neman a dage ranar daga 2 ga watan Nuwamba zuwa 16 ga watan Nuwamban.

” Mutane, dattawa da gwamnatin jihar Bayelsa sun mika kukan su ga hukumar zabe da ta canja ranar raben gwamna na jihar saboda a wannan rana ne suka bukin godiya ga Allah, da ya ke cikin kundin dokokin jihar.

” A dalilin haka kuwa sai muka ga ya dace mu girmama wannan raba ta su mu dage zaben zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Wannan dage zabe ya shafi jihar Kogi da dama a rana daya za a yi zaben gwanan jihar.

Share.

game da Author