Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta kafa kwamiti domin yin kididdigar yawan adadin yawan mata da yara kananan ke mutuwa a kasan nan.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yace gwamnati ta yi haka ne domin shawo kan matsalar yawan mace-macen yara kanana da mata da ake fama da shi a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa mata 145 masu shekaru 15 zuwa 45 ne suke mutuwa a dalilin matsalolin haihuwa.
Sannan duk rana yara 2,300 ‘yan kasa da shekara biyar ne ke mutuwa a dalilin kamuwa da cututtukan da za a iya kawar wa.
Bayan haka shugaban cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa (NPHCDA) Faisal Shu’abu ya ce gwamnatin tarayya ta amince ta bude fannin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana a kasar na.
Yace cibiyar su za ta hada hannu da cibiyar kawar da cutar shan inna na kasa domin samun kudaden da za a bukata wajen ganin an samu nasara a akai.
Faisal ya kuma ce fannin za ta hada hannu da sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki, kungiyoyin bada tallafi da sauran mutane domin karkato da hankulansu wajen mahimmancin mara wa wannan buri baya.