Gwamnatin Filato za ta ruguje kuma ta kone Babbar Kasuwar Jos ran 19 Ga Mayu

0

Gwamnatin Jihar Filato ta bada sanarwar cewa a ranar 19 Ga Mayu, za ta rushe tare da kone wani sashe na Kasuwar Jos.

Wannan sanarwa ta fito daga bakin Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Filato, Yakubu Datti.

Sannan kuma sanarwar ta shawarci wadanda duk ke zaune mita 200 daga kasuwar su gaggauta ficewa nan da ranar 17 Ga Mayu kafin karfe 6 na yamma.

“Za a hana zirga-zirgar ababen hawa a dukkan hanyoyin da suka doshi kasuwar, kuma za a rufe su, saboda tabbatar da tsaron rakuya da dukiyoyin jama’a.

“Gwamnati na bada hakuri kan duk wata takuwarawa da jama’a za su fuskanta sakamakon wannan gagarimin aiki da za a yi.” Inji Datti.

Ya kuma kara jaddada aniyar Gwamna Simon Laong na ganin ya sake gina Babbar Kasuwar ta Jos.

Datti ya kara nanata cewa gwamnati na ci gaba da daukar dukkan wasu matakai da suka wajaba, domin ganin an sake gina kasuwar a cikin yanayin da jama’a ba su tagayyara ba.

Share.

game da Author