Gwamnatin Da Tafi Kowacce Kyau, Itace Take Samar Wa Da Talaka Farin Ciki, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Tsakani da Allah, bambancin da yake tsakanin mulkin siyasa da mulkin da ba na siyasa ba shine samar da gagarumin farin ciki a cikin al’umma masu rinjaye kamar yadda John S. Mills yace.

Misali, ana iya gane ingancin mulkin siyasa ne a lokacin da talakawa masu rinjaye suke farin ciki dashi.

Mafi girman kuncin rayuwa shine talaka ya rasa abinci, abinci shine bukatar dan Adam ta farko a duniya, yana da mahimmanci sosai a rayuwar mutane shiyasa suke shiga cikin mu’amila iri-iri don su same shi. Kamar yadda Karl Marx yace.

Tarihi ya nuna cewa, tun kafin zuwan gwaunati, mutane suna shiga daji su farauto abun da zasu ci, domin ko bayan zuwan gwaunati ma, amfaninta shine ta bawa mutane kariya ( Protection/security).

Tabbas neman kariya (protection) ne yasa mutane suka sallama kansu ga gwaunati kamar yadda yake a cikin nazariyar J.J Rousseau (Theory of social contract).

Dudley Seers (1979) yace, duk sanda kakeso ka fahimci cigaban arzikin kasa, dole ka nemi amsoshin wadannan tambayoyin guda uku :-

1. Menene matsayin talauci a kasar?

2. Menene matsayin rashin aikin yi?

3. Menene matsayin rashin daidaito ‘unequality’?

Alhamdulillah! Tunda yanzu gwamnati ta gamsu da cewa kasar Najeriya ta fita daga faduwar tattalin arziki (recession), tabbas akwai bukatar a samu canji a rayuwar talaka.

Gaskiya mafi yawancin talakawa karfin hali suke, ba don suna jin dadin wasu ‘Manufofi da shirye-shiryen gwamnati ba, kuma wani babban abun sha’awa shine har yanzu wasu suna nan da soyayyar gwamnatin a zuciyarsu.

Shugaba Buhari ya samu babbar shaidar kasancewa mai gaskiya a wajen talakawan Najeriya kuma har yanzu wasu daga cikin al’umma suna nan da wannan akidar. Wannan itace babbar ribar da ya samu a siyasance.

Kalmar “Mai gaskiya” itace ta kai shi ga kujerar shugabancin Najeriya cikin amincewar Allah.

Akwai bukatar ayi amfani da kujerer siyasa wajen saka farin ciki a zukatan mutane. Gwamnatin gaske tana kokari ne ta samar da abun da ko bayan ta gama mulki wasu zasu dinga tunata da shi.

Duk irin kokarin da za ayi ba zai gamsar ba idan gwaunati ba ta samar da sauki a rayuwar talakawa ba. Lallai sai da ruwan ciki ake jan na rijiya.

Nayi wannan rubutun ne a matsayina na wanda ba kowa ba kuma ba yaron kowa ba a cikin ‘yan siyasar Najeriya.

Ina rubuce rubuce ne don na sanar da al’umma ‘dan abun da na sani a matsayina na jaririn dalibin kimiyar siyasa, gaskiya bana rubutu don na farantawa wani dan siyasa. Lallai Allah shaida ne akan haka.

Shiyasa nake burin ‘yan Najeriya zasu yi min adalci idan sun karanta wannan rubutun.

Allah ya shiryar damu.

Comrade M.K Soron Dinki

Share.

game da Author