Gwamnati ta ragargaji Obasanjo a kan furucin sa game da Boko Haram

0

Gwamnatin Tarayya ta ragargaji Shugaba Olusegun Obasanjo, dangane da furucin da yayi kwanan nan a kan Boko Haram.

An ruwaito Obasanjo yace, “ Batun Boko Haram tuni ya tashi daga matsalar rashin ilmi da rashin aikin yi a tsakanin matasa, kamar yadda aka rika fassara shi a baya.

“Yanzu ya koma yunkuri ne na fifita Fulani a fadin Afrika ta Yamma tare da kafa musulunci ta hanyar aikata mugayen laifuka da suka hada da damfara, safarar mutane, safarar kwayoyi, safarar bindigogi, hakar ma’adinai.”

Haka aka ruwaito Obasanjo ya furta a cikin coci.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta ruwaito martanin da Sule Lamido, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma tsohon minista ya mai da masa raddin cewa kamata ya yi a tsaya a matsayin sa na dattijo kuma uban kasa, maimakon darsasa kabilanci da addinanci a zuciyar sa.

Yau Talata kuma gwamnatin tarayya ta shiga sahun wadanda suka soki lamirin Obasanjo, inda ta nemi yayi shiru, domin kalaman sa na iya ruruta kabilanci da addinanci.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne bayyana haka a cikin wani bayanin da ya fitar ga manema labarai.

A baya Obasanjo ya taba yin wani yunkuri na kawo karshen Boko Haram. Har jagaban zaman tattauna sulhu ya taba yi tsakanin Boko Haram da Gwamnatin Goodluck Jonathan.

Irin rikon-sakainar-kashin da Obasanjo ya fahimci gwamnatin Jonathan ta yi wa Boko Haram ne ya sa ya ki goyon bayan sake zaben sa, ya goyi bayan Buhari a zaben 2015.

Tun da Obasanjo ya koma ya na cakkakar gwamnatin Buhari, har yaki goyon bayan ta karara a zaben 2019, ita ma gwamnatin ba ta kara raga masa ba.

Lai Mohammed ya ce furucin da Obasanjo ya yi a coci cike ya ke da ruruta wutar kabilanci da addinanci, musamman yadda ya jingina batun Boko Haram da addini

Gwamnati ta ce kalamai ba irin wanda suka kamata su fito ga dattijo kuma tsohon shugaban kasa, kamar Obasanjo ba.

“Wannan ai wani bala’i ne a ce mutumin da ya shiga fagen fama ya fafata yakin hana Najeriya tarwatsewa, a ce kuma yanzu tsofai-tsofai da shi ya dawo ya na ruruta kabilanci da addininanci.

Lai ya ce Boko Haram da ISWAP kungiyoyin ta’adda ne, kuma su babu ruwan su da ware dan wani addini, kowa suke kashewa.

“Tun daga lokacin da Boko Haram ya fara kunno kai a zamanin mulkin Obasanjo, har ya yi muni cikin 2009, sun kashe musulmi masu dimbin yawa fiye da dukkan sauran mabiyan wasu addinai baki daya.

“Abin takaice ne kenan har a fito a ce Boko Haram shiri ne na musuluntar da Najeriya, ko dora Fulani a kan sauran kabilun kasar nan wai har ma da na Afrika ta Yamma.

Sanarwar ta kuma ci gaba da nuna irin kokarin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika yi wajen kawar da Boko Haram tun daga hawan sa mulki cikin 2015.

Share.

game da Author