Masu zaman gudun hijra a sansanin Kuchingoro, babban birnin tarayya Abuja sun koka kan yadda gwamnati ta ti watsi dasu kamar ba mutane ba.
Shugaban sansanin Philemon Emmanuel ta bayyana haka ne a ziyarar da kungiyar ‘Kings College Old Boys Association (KCOBA) suka kai sansanin a farkon wannan mako.
Philemon ta ce suka samu talklafi ne daga kungiyoyi masu zaman kansu amma ba daga gwamnati ba.
Idan ba a manta ba a 2014 ne gwamnati ta kafa sansanin Kuchingoro domin samar wa ‘yan gudun hijira daga karamar hukumar Goza a jihar Barno mafaka.
Sai dai kuma bayan dan wani lokaci gwamnati ta sanar wa wadannan mutane cewa su koma garuruwan su cewa an ci karfin Boko Haram da su ka fatattake su a wancan lokacin. Wasu da dama daga cikin yan gudun hijra basu koma ba sun ci gaba da zama a sansanin.
A cikin sansanin akwai rijiyar burtsatse dake amfani da hasken rana, asibiti daya, da makaranta daya wanda kungiyoyi masu zaman kan su da uwargidan tsohon ministan Abuja Bala Mohammed suka samar wa masu zama a sansanin.
Da take tofa albarkacin bakinta shugaban kungiyar matan sansanin Ladi Mathias ta bayyana cewa tana sana’ar soya kosai ne da noma tunda ta zo wannan sansani.
” A kullum rana sai na kashe Naira 4000 kudin motar zuwa gonata dake jihar Nasarawa daga nan sannan duk ranar da zan fita dole mijina ke zama a gida domin kula da yara.
Shugaban kungiyar Tsuffin daliban KCOBA Emmanuel Mogbolu ya bayyana cewa kungiyar ta ziyarci sansanin ne domin tallafa wa mazauna sansanin.