GARKUWA DA MUTANE: Ba mu yi wa Kungiyar Miyetti Allah tayin naira bilyan 100 ba –Sufeto Janar

0

Sufeto Janar Mohammed Adamu, ya karya ji-ta-ji-tar da ake ya watsawa a soshiyal midiya cewa gwamnatin tarayya ta yi wa Kungiyiyar Miyetti Allah tayin naira bilyan 100 domin Fulani su daina hare-hare da garkuwa da mutane.

Adamu ya karya wannan zargin jiya Talata, a Abuja, a lokacin da ya ke magana da manema labarai bayan kammala ganawar tsawon sa’o’i biyu da Majalisar Dattawa.

Yayin da aka fara baza labarin, kungiyar HURIWA ta nuna bacin rai a kan zargin tare da cewa idan aka bayar da kudaden, to babban laifi ne gwamnatin tarayya ta aikata.

Sufeto Janar ya ce wannan magana ba ta ma taso ba, kuma idan ma batun dakile masu garkuwac da mutane ne, to ba da kudi za a kawo karshen su ba.

Ya ce abin da wasu suka yada a soshiyal midiya, kirkirar karairayi ne kawai, amma ba gaskiya ba ne, karya ce domin karkatar da hankulan mutane.

“Magana ce wadda ba ta da tushe, kuma babu wannan zance, kuma ba a yi wani tason sirri da kungiyar Miyetti Allah ba.”

An yi masa tambaya dangane da zargin fyaden da ‘yan sanda suka yi wa wasu da ake zargi karuwai ne a Aabuja, sai Adamu ya ce an kafa kwamitin bincike, wanda zai bayyana yadda gaskiyar abin ya ke.

Sai ya ce kuma ya na tabbatar da duk dan sandan da aka kama da laifi, to za a hukunta shi. ko ma wane ne.

Share.

game da Author