Shugaba Muhammadu Buhari nuna damuwar sa a kan yadda manyan masu ilmin kasar nan da masu ruwa da tsaki suka kasa shawo kan matsalar kuncin rayuwa da samanar da ilmi ga milyoyin marasa karfi a cikin al’umma.
Ya nuna wannan damuwar ce a lokacin da ya karbi bakuncin shan ruwa daga Mataimakin sa Yemi Osinbajo, ministoci, shugabannin tsaro na sojoji da na sauran hukumomin tsaro da manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya suka kai fadar sa.
Buhari ya ce hankalin sa ya kan tashi matuka ganin irin halin kuncin rayuwa da ake fama da shi a kasar nan.
Daga nan sai ya kalubalanci manyan masu ilmi da su gaggauta fito da tsarin da zai sassauta wa al’umma wannan halin kuncin da suke ciki.
Ya ce tuni dai a na ta bangaren, gwamnatin tarayya ta bijoro da tsarin ciyar da ‘yan makarantar firamare da kuma ‘Trader Moni’, domin rage wa al’umma radadin talauci a fadin kasar nan.
Buhari ya jinjina wa Osinbajo a bisa rawar ganin da ya yi wajen ganin samun nasarar shirin ‘Trader Moni.’
“Idan ina kewayawa cikin kasar nan, abin da ke tayar min da hankali da bata min rai babu kamar ganin irin halin kuncin da talakawa ke ciki. Za ka ga yaro dan almajiri sanye da yagaggun kaya, ga kwanon roba a hannun sa. Ya na neman abin da zai ci.
“Su maganar ilmi a wajen su wata ni’ima ce ta musammanan, domin abinci ne a gaban su tukunna. Ni ina ganin dukkan mu mun gaza, saboda ina ganin ya kamata mu fito da wani shiri da zai samar da ingantaccen ilmi ga yaran mu kanana komai talaucin da su ko iyayen su ke fama da shi.
“Don haka ina godiya ga mataimakin shugaban kasa da ya shigo da tsarin ciyar da yara ‘yan makaranta da kuma “Trader Moni.
“Amma fa a gaskiya wasun mu a al’adance ba su da imani. Babu ruwan mu da abin da ke damun wasun mu. Idan jifa ta wuce kan mu, ta fada kan kowa kenan.
“Har cewa Osinbajo na yi ya fa rika yin kaffa-kaffa a shirin ‘Trader Momi’ din nan, kada a danne shi a tsakiyar kasuwa. Musamman da na rika ganin dirka-dirkan mata su na kewaye shi.
“Da farko da ban maida kai ga shirin “Trader Moni’ ba, amma da na rika ganin yadda aka dauke shi da muhimmanci, sai na rika jin dadi da shirin matuka.
“Kuma a gaskiya akwai tsare-tsare da yawa da aka gudanar, wadanda shi Mataimakin Shugaban Kasa ne ma ke fara yin tunanin aiwatar da su, kafin hankalin na ya kai a gare su.
“To amma ya san ni sosai. Idan ya ce ga abin da za a yi ni kuma na nuna a’a, sai ya tirje ya ce yin abin ya fi rashin yin sa amfani. Sai na kan ce masa to je ka yi abin da ka ke so ka yi. Kuma idan ya yi, sai ka ga abin ya na da muhimmanci soasai.
Mutane da yawa cikin har da Mataimakin Shugaban Kasa sun yi jawabai a wurin buda-bakin da aka yi jiya Lirtinin a ranar azumi na takwas.