Gangamin Kalubalantar Ganduje! Daga Imam Murtadha Gusau

0

Gangamin Kalubalantar Ganduje Gandun Sharri! Daga Imam Murtadha Gusau

Laraba, Ramadan 10, 1440 AH (Mayu 15, 2019)

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwana masu girma! A gaskiya yanzu na dan fara samun sa’ida, yanzu na dan fara nunfasawa, yanzu na dan fara jin dadi, yanzu hankalina ya dan fara kwanciya, yanzu ne na kara yarda da amincewa da sakankancewa cewa lallai duk da abubuwan da suke faruwa a arewa, na rashin tsaro, har yanzu arewa tana da karfi, kuma tana da manyan bayin Allah, kuma masu yi don Allah, da na samu labarin cewa manya, bayin Allah, mutanen kirki, masu son ci gaban arewa da Musulunci, masu kaunar hadin kan al’ummah, sun fara yunkurin daukar mataki a kan gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da yake kokarin ya mayar da mu baya, yake kokarin ya kara jefa yankin arewa cikin wani sabon shafi na rarraba kan jama’ah da tarwatsa al’ummah, domin cimma wata manufa tasa ta siyasa, ba domin ci gaban talakawan Kano ba.

Allah ya saka wa manyan dattawan Kano da alkhairi, Allah ya saka wa Sarkin Musulmi Mai Alfarma Muhammadu Sa’ad Abubakar da alkhairi, Allah ya biya su da gidan Aljannah, amin.

‘Yan uwa, wallahi wannan yunkuri na su abin a yaba ne kwarai da gaske, haka ake son manya suyi, wato suyi kokarin taka wa duk wani shedani burki, mai kokarin mayar muna da hannun agogo baya, mai kokarin rusa al’ummah! Ta yaya wani dan siyasa, marar kishin al’ummar sa, marar girmama addininsa da al’adunsa, marar ganin girman manya, zai buwaye su? Kawai don Allah ya dan ba shi aron mulki na ‘yan wasu shekaru, amma yazo yana kokarin rusa muna abinda iyayen mu da kakannin mu da malaman mu da mujahidan mu suka gina muna shekaru aru-aru da muke tinkaho da shi kuma muke alfahari da shi?

Wai kuma don rashin kunya, mai wannan aikin har wasu suke kokarin kiran sa wai “KHADIMUL ISLAM”? Ta yaya za’ayi mai kokarin rusa addinin Musulunci da abinda Musulunci ya assasa kuma ya zama khadiminsa? Idan ba an mayar da mutane jahilai ba?

Haba jama’ah! Wai don Allah waye Ganduje? Ai abun kunya ne ma wallahi a wurin manyan arewa ace wannan mutum ya buwaye su! Shi din wa? Haba, ai wallahi wargi wuri yake samu!

Ina rokon Allah ya taimaki manyan mu, ya basu sa’a da nasara a kan wannan yunkuri na alkhairi, amin.

A gaskiya kuma wajibin mu ne mu san cewa wannan yunkuri nasu shine daidai, kuma shine rufin asirin mu. Domin wallahi yancin mu da mutuncin mu da martabar addinin mu da al’adunmu suke kokarin kwato muna, don haka wajibi ne muyi masu addu’a da fatan Allah ya taimake su!

Haba ‘yan uwa, wai ace wannan mutum Ganduje rashin kunyar ta sa ta kai har ga ya raina muna Sarkin Musulmi? Wanda wallahi idan ka raina shi ka raina addinin mu? Wai ace wai wannan mutum yaki ya girmama Sultan, haba! To idan ka wulakanta muna wadannan mutane, waye kuma yayi saura? So muke yi irin wulakanci da cin mutuncin da arna, turawa, ‘yan mulkin mallaka, mashaya giya, wawaye, jahilai, suka yiwa sarakunan mu da addinin mu wani dan siyasa, karen farautar turawa yaci gaba da shi, kuma mu sa masa ido? Wallahi ba zai taba yiwuwa ba!

Ku sani, wallahi, wannan mutum, Ganduje gandun sharri, idan ba mataki kwakkwara aka dauka a kan sa da ire-iren sa ba, wallahi za su ci gaba da wulakanta muna sarakuna iyayen al’ummah.

Ya manta cewa, wadannan bayin Allah, wato sarakuna, jagororin addinin mu ne da al’adunmu? Ya manta cewa, jihadin Shehu Dan Fodio ne ya kawo su, kuma shine ya assasa wadannan kujerun? Bai san cewa idan an wulakanta sarakuna, addinin mu da al’adun mu ne ake nema a rusa ba? Wallahi, wannan yaki ne da ya kamata duk wani dan halak, mai kishin addinin mu da al’adun mu da arewar mu ya shiga ayi da shi. Domin mu sani, da an rusa muna sarakunan mu, an raina su, to shike nan, bamu da wani katabus kuma, kuma bamu da wani abu da kuma ya rage da zamu yi tinkaho da shi.

Wannan al’amarin, al’amari ne da ya kamata mu sani cewa, Ganduje fa ba wai kawai da Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II yake fada ba, a’a da dukkanin mu ‘yan arewa, Musulmai yake fada. Don haka, ya zama wajibi a gare mu, mu hadu mu yake shi domin mu dawo da martabar mu da mutuncin mu. Yin haka shi zai sa duk wani wawan dan siyasa da giyar mulki ta ke dibar sa, ya ke kokarin tozarta muna iyayen mu, wato sarakuna, zai san da cewa, bai fa isa yaci mutuncin su ya zauna lafiya ba!

Wadannan mutane, masu kokarin raina muna shugabanni da sunan siyasa, ya kamata su sani, wallahi, dukkanin sarakunan mu, tun daga Sarkin Musulmi, har zuwa Shehun Borno, har zuwa Sarkin Gwandu, har zuwa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, har zuwa Sarkin Gombe da Sarkin Suleja…kai da duk ko wane sarki da kuka sani, shugabanni ne na addinin Musulunci, jagororin mu ne na addini. Don haka taba su taba addinin Musulunci ne.

Muna daukar wulakantasu, wulakanta addini ne. Cin mutuncin su, cin mutuncin addini ne. Don haka, wallahi, ya kamata wawayen ‘yan siyasa, jahilai, da magoya bayan su, da ‘yan koren su, basu yi masu banbadanci, su kiyaye wannan. Kuma su iya sani cewa, ba zamu taba zuba ido, muyi shiru, mu rungume hannuwa, muna kallo, ana cin mutuncin jagororin addinin mu da al’adunmu mu kyale su ba. Domin zubar da mutuncin wadannan bayin Allah, wallahi zubar da mutuncin addinin Musulunci ne! Domin idan ma har kana da wani sabani da su (personal grudges), to kujerarsu da asalin kujerar zaka kalla ba su ba!

Don haka ya zama wajibi mu kiyaye!

Ina rokon Allah yaja zamanin sarakunan mu baki daya, Allah ya kara kare mutuncin su da imanin su da kujerun su, Allah ya isar masu ga duk wani mutum mai neman cin zarafin su, amin.

Ina rokon Allah ya taimake su, yayi masu jagora da kariya, ya kare mutuncin su da kujerun su daga wawanci da shirmen wawaye, mahassada, makirai, magauta da jahilai, amin.

Ya kamata Ganduje da duk wani dan siyasa da ke son farraka al’ummah, ya kawo masu rarrabuwa da rikici da gaba, a lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama’a a karkashin mulkinsa. Jama’ar da suke zaune a kauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su. Daga baya ne da garuruwan suka fara bunkasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke kara inganta, a lokacin ne aka samu shugaba guda daya da ya hada kan mutane, shine Sarkin Kano.

Sannan ya kamata Ganduje da duk wani dan siyasa da ba ya son al’ummah su zauna lafiya, cikin hadin kai da kaunar juna, su sani, ita wannan masarauta ta Kano tana cikin manyan masarautu a kasar Hausa a yammacin Afirka. Kuma tarihi ya nuna cewa tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun zamanin jahiliyya kafin ma zuwan addinin Musulunci. Kuma wannan masarauta ta taimaka sosai wurin bunkasa garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya. Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya da jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da garin, don haka cin mutuncin wannan masarauta, cin mutuncin jama’ar Kano ne baki-daya.

Kuma ya kamata mu sani, shi sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ikon Allah ne, Allah ne ya kawo shi, Allah ne ya dora shi akan wannan kujera, ba shine ya dora kan sa ba. Don haka wallahi, duk wanda yace zai ja dashi, to zai ja da ikon Allah ne! Sarki Muhammadu Sanusi II shine na 57 a jerin sarakunan Kano, kuma na 14 a jerin sarakunan Fulani.

An nada shi sarkin Kano bayan mutuwar Sarki marigayi Alhaji Ado Bayero.

Malam Muhammadu Sanusi II jikan Sarkin Kano Sanusi I ne. Maihaifinsa Aminu Sanusi yayi Chiroman Kano. Allah ya gafarta masu, amin.

Kuma binciken masana ya nuna cewa shine sarkin Kano da ya fi magabatansa ilimin zamani, sannan kuma yana da ilimin addinin Musulunci.

Kwararren masanin tattalin arziki ne, kuma kwararren ma’aikacin banki, inda ya taba rike mukamin gwamnan Babban Bankin Najeriya, wato CBN.

An sauke shi daga mukamin gwamnan CBN saboda yadda yake sukar gwamnatin Goodluck Jonathan da mulkinsa a lokacin, domin shi mutum ne da baya iya yin shiru idan ya ga cewa ana kokarin zaluntar al’ummah.

An haifi Malam Muhammadu Sanusi II a ranar 31 ga watan Yulin 1961. Kuma an nada shi Sarkin Kano ranar Lahadi 8 ga watan Yuni 2014.

Ina rokon Allah ya taimake shi, ya dora shi a saman makiyansa da magautan sa, da dukkan masu yi masa makirci, ya taya shi riko, ya kara masa imani da son talakawan sa, amin.

Wassalamu Alaikum

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author