Ganduje zai aurar da zawarawa 1500 a rana daya

0

A yau Asabar ne Gwamnatin Jihar Kano ta shirya aurar da zawarawa har 1,500 a fadin kananan hukumomin Kano 44.

Sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na gwamna, Abba Anwar ya fitar, ta nuna cewa a yau Asabar ne za a daura aure a dukkan fadin kananan hukumomin jihar.

Anwar ya ce gwamnatin Kano ce za ta biya kudin sadakin kowace naira 20,000 a lokacin daurin auren.

Ya ce za a biya kudin ‘lakadan’ ba ‘ajalan’ ba.

Wannan gagarimin auren zai ci naira miliyan 30, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sannan kuma gwamnatin ce za ta sai wa amaren kado, kafita, da sauran kayan dakin amare da suka hada har da kujeru na kushin. Su kuma an guna an shirya raba musu shaddar da za su yi ankon biki a ranar daurin auren na su.

Gwamnatin Jihar Kano ta dade ta na shirya wannan al’ada ta aurad da zawarawa da nufin rage yawaitar zawarawa a fadin jihar. Wannan ya samo asali ne tun zamanin mulkin tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso da Ibrahim Shekarau.

An rika shirya auren a karkashin Hukumar Hisba ta Jihar Kano.

Share.

game da Author